BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Lyanco: Dan kwallon Brazil ya koma Southampton daga Torino

 120248160 Lyanco Southampton ta kammala daukar dan kwallon Brazil, Lyanco

Thu, 26 Aug 2021 Source: BBC

Southampton ta kammala daukar dan kwallon Brazil, Lyanco kan yarjejeniyar kaka hudu daga Torino.

Jaridun Italiya da na Birtaniya sun wallafa cewar kudin cinikin dan wasan mai tsaron baya ya kai fam miliyan 6.4.

Lyanco, mai shekara 24, wanda ya koma Torino a 2017, ya yi wasa 53 a dukkan karawar da ya yi mata, ya kuma je aro a Bologna a 2019.

Dan kwallon Brazil zai kara karfin kungiyar da Ralph Hasenhuettl ke jan ragama, bayan da mai tsaron bayanta dan wasan tawagar Denmark, Jannik Vestergaard ya koma taka leda a Leicester City a farkon watan nan.

Lyanco ya zama na shida da Hasenhuettl ya dauka a kakar bana, bayan Theo Walcott da Romain Perraud da Tino Livramento da Adam Armstrong da kuma Thierry Small.

Southampton, wadda keda maki daya daga wasa biyu a Premier League a bana, za ta ziyarci Newport County a League Cup ranar Alhamis..



Read full article

Source: BBC