BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Man City 5-0 Arsenal: Arsenal tana ta karshe a teburin Premier League

 120317309 Artetacoro Kocin Arsenal Mikel Arteta

Sun, 29 Aug 2021 Source: BBC

Manchester City ta doke Arsenal da ci 5-0 a wasan mako na uku a Premier League a Etihad ranar Asabar.

Tun kan hutu City ta zura kwallo uku a ragar Gunners ta hannun Ilkay Gundogan da Ferran Torres da Gabriel Jesus.

Wannan shine karo na biyu da aka ci Arsenal kwallo uku ko fiye da hakan tun kan hutu, bayan 4-0 da Chelsea ta yi mata a Maris din 2014 aka doke Gunners 6-0 a karawar.

Saura minti 10 su je hutu aka bai wa dan kwallon Arsenal, Granit Xhaka jan kati, kuma karo na hudu da ake korar sa daga wasa tun daga 2016/17.

'Yan wasan da aka bai wa jan kati hudu a Premier League bayan Xhaka tun daga 2016/17 sun hada da Fernandinho da kuma David Luiz.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta kara biyu a ragar Arsenal ta hannun Rodrigo Hernandez da kuma Ferran Torres, wanda ya ci biyu a gumurzun.

Wannan shine karon farko da Arsenal ta kasa cin wasa a karawa uku da fara kakar Premier League tun bayan 1954/55.

City ta zama ta uku da ta zura kwallo 10 a raga a wasa biyu a gida da fara Premier League a kakar tamaula, bayan Arsenal da ta yi wannanbajintar a 2010/11 ta ci 10 da Manchester United da ta zura 11 a raga a 2011/12.

Arsenal ta zama ta biyu da ta yi rashin nasara a wasa uku da fara kakar Premier da aka zura mata kwallo tara a raga, Bayan Wolverhampton Wanderers a 2003/04.

Bayan da aka fara wasan mako na uku da aka doke Arsenal a City, Gunners tana ta karshe a kasan teburi da kwallo tara a raga, ita kuwa ba ta ci ko daya ba.

Brentford ce ta fara doke Arsenal 2-0 a wasan makon farko a kakar bana, sannan Chelsea ta zura kwallo 2-0 a ragar Gunners a Emirates.



Read full article

Source: BBC