BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Man United: Wa zai horar da United tsakanin Pochettino da Erik ten Hag?

 123995130 Mediaitem123995126 Kocin PSG, Mauricio Pochettino tare da kocin Ajax Erik ten Hag

Mon, 4 Apr 2022 Source: BBC

Manchester United ta tashi 1-1 da Leicester City a wasan mako na 30 a gasar Premier League da suka kara ranar Asabar.

Leicester City ce ta fara cin kwallo ta hannun Kelechi Iheanacho, minti uku tsakani United ta farke ta hannun Fred.

Kawo yanzu United ta koma ta bakwai a teburin Premier League da maki 51, bayan wasa 30, wadda ke neman gurbin shiga gasar Zakarun Turai a badi, bayan da ta kasa kai bantenta a bana.

Kungiyar Old Trafford ta nada Ralf Rangnick a matakin kocin rikon kwarya, wanda har yanzu bata sauya zani ba, bayan da ya ci wasa tara daga 21 da ya ja ragama, tun bayan da ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a watan nuwamba, wanda ya yi nasara a karawa bakwai daga wasa 17.

United na bukatar maki 14 a wasa takwas da ke gabanta kan karkare kakar bana, domin ta haura 64 da ta samu a kakar 2013-14 karkashin David Moyes, wadda itace mafi muni da kungiyar ta yi a shekara 10.

Kungiyar Old Trafford na kokarin ganin ta dauko mai horarwa kwararre da zai fitar da ita daga halin da take ciki, kuma kawo yanzu ana maganar Erik ten Hag da kuma Mauricio Pochettino.

To sai dai kuma batun da wasu ke magana shine idan United ba ta kai ga daukar daya daga cikinsu ba, wa za ta koma nema?

Shi dai Luis Enrique baya cikin tsarin , wanda ke jan ragamar tawagar Sipaniya, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen Disamba, watakila ya tsawaita zamansa, ganin rawar da yake takawa.

Haka kuma ana hangen abun da ke faruwa a Chelsea, wadda ake neman mai saya, watakila kungiyar ta nemi sabon koci, watakila ta yi kokarin taya Thomas Tuchel, kila kuma dan kasar Jamus ya ci gaba da aiki a Stamford Bridge.

United na son tuntubar dukkan kociyoyin biyu, sai dai ta kwan da sanin abin zai yi dan karen wahala.

Watakila United ta taya mai horar da Sevilla, Julen Lopetegui, amma kila ta tuntubi Brendan Rodgers, wanda ya taka rawar gani a Liverpool da kuma Leicester City da yake horarwa a yanzu.

Amma dai ana ganin United za ta fi maida hankali wajen kokarin daukar daya daga tsakanin Ten Hag ko kuma Pochettino.



Read full article

Source: BBC