BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Man United za ta sayar da 'yan wasa bakwai a Janairu

 116507762 Gettyimages 1227927505 Jesse Lingard, dan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila

Sun, 19 Sep 2021 Source: BBC

Manchester United na shirin sayar da 'yan wasanta bakwai a watan Janairun 2022, idan an bude kasuwar 'yan kwallo ta Turai.

Ranar 1 ga watan Janairun 2022 za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a wasu kasashen Turai ta bana.

United ta tara 'yan wasa da yawa da ya zama wajibi ta rabu da wasu, idan ba haka ba biyan albashi zai iya jefa ta cikin matsin tattalin arziki.

Kamar yadda The Sun ta wallafa, United za ta sa 'yan wasa a kasuwa a watan Janairu da suka hada da Donny van de Beek da Jesse Lingard da Phil Jones da Eric Bailly da Anthony Martial da Diogo Dalot da kuma Alex Telles.

Haka kuma kungiyar za ta bayar da aron matasan 'yan wasanta wadanda ke kan ganiya ga wasu kungiyoyin domin su kara samun kwarewa a fagen taka leda.

Sai dai kuma United na fama da kalubalen rarrashin Paul Pogba ya ci gaba da taka leda a Old Trafford, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar badi.

Pogba dan wasa ne da kungiyoyi ke son zawarcinsa, ciki har da tsohuwar kungiyarsa Juventus da Real Madrid da Paris St Germain in ji wasu rahotannin.

Sai dai kuma sunan Jesse Lingard cikin wadanda United za ta sayar a Janairu ya zo da mamaki, bayan da Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewar yana son matashin dan wasan Ingila ya ci gaba da zama a Old Trafford.

Lingard wanda ya ci wa United kwallo na biyu a karawar da ta doke West Ham United ranar Lahadi a gasar Premier League, zai iya tattaunawa da wasu kungiyoyin a Janairu, bayan da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana.

United ta yi ta yi wa Lingard tayin tsawaita kwantiraginsa a Old Trafford amma yana ki, wanda ke tunanin ba za ta dunga saka shi a wasanni ba, musamman da Cristiano Ronaldo ya koma kungiyar a bana.

Lingard ya taka rawar gani a West Ham United a bara da ya buga wasannin aro, har ya kai kungiyar gurbin buga gasar Zakarun Turai ta bana.



Read full article

Source: BBC