BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Manchester City vs Real Madrid: Real ta sauka a Ingila don buga Champions

 124285105 Mediaitem124285101 Wasu yan wasan Real Madrid

Mon, 25 Apr 2022 Source: BBC

Real Madrid ta ziyarci Ingila, domin buga wasan daf da karshe zangon farko a Champions League da za ta fafata da Manchester City ranar Talata.

Madrid ta taso daga Sifaniya ta filin jirgin sama na Adolfo Suarez Madrid-Barajas ta kuma sauka lafiya tare da jami'ai da 'yan wasanta.

Bayan da ta sauka a Manchester sai ta wuce masuki, wato otal da ake kira Hyatt Regency, inda za ta zauna har bayan wasan na hamayya.

Manchester City wadda ba ta taba daukar Champions League ba, za ta kece raini da Real Madrid mai 13 jumulla, ita ce kan gaba a yawan lashe Champions League.

Real Madrid ta kawo wannan matakin a gasar ta Zakarun Turai ta bana, bayan da ta fitar da mai rike da kofi, Chelsea.

Ita kuwa City ta yi nasara a kan Atletico Madrid ta Sifaniya, bayan da ta ci 1-0 a Etihad, sannan suka tashi 0-0 a gidan Atletico a wasa na biyu.

Wannan shi ne wasa na bakwai da za su kece raini a tsakaninsu a Champions League, kowacce ta yi nasara a karawa biyu da canjaras biyu.



Read full article

Source: BBC