BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Manchester United ta sanar da asarar £115.5m a kakar 2021-22

432d4ed0 3a79 11ed 9ae9 959994b8a64c Erik ten Hag

Thu, 22 Sep 2022 Source: BBC

Manchester United ta sanar da asarar da ta £115.5m a kakar 2021-22, duk da kuma kudin shigarta ya karu da kashi 18 zuwa £583.2m.

Kungiyar ta bayyana asarar ne a bayanan da take fitarwa na hada-hadar kudinta a karshen shekara a watan Yuni, wanda ya nuna asarar ta karu zuwa £23.3m idan aka kwatanta da wadda ta yi a 2021.

Bashiun da ake bin kungiyar shi ma ya karu, daga £419.5m a 2021 zuwa £514.9m a wannan shekarar, ya karu da sama da kashi 22.

"Abin da kungiyar ta sanya a gaba shi ne ta yi nasa a wasanni ta kuma nishadantar da magoya bayanmu," in shi shugaban Richard Arnold.

"Sakamakon 'yan wasan da muka dauka a bara irinsu Cristiano Ronaldo da Jadon Sancho da kuma Raphael Varane albashi ya karu da kashi 19.1m, yanzu ya koma £616.6m daga £384.2m".

Wannan ne adadi mafi yawa da aka samu a tarihin Premeir, ya wuce na Manchester City na baya da yakai £355m

"Sakamakon da muka samu a 2022 na kudi, ya nuna muna warwarewa daga matsalar annobar korona, cikakkiyar dawowar magoya baya da kuma kara sanya kudin abokan hulda ga tawagarmu," in ji Cliff Baty.

"Rashin fita wasannin karshen kaka da muka yi zuwa wasu kasashen a 2021, ya kara yawan abubuwan da muke kashewa."

Kudin da aka biya tsohon kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer wanda aka kora a watan Nuwamba 2021, da maganar Ralf Rangnick wanda ya rike kungiyar na rikon kwarya da sauran tawagarsa sun hada £24.7m.



Read full article

Source: BBC