BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Matakai bakwai da aka dauka a Zamfara domin magance matsalar tsaro

 120326671 7be3b5b2 A777 4453 A1ae 1466bf92c785 Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle

Mon, 30 Aug 2021 Source: BBC

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ayyana daukar matakai bakwai da ta ce za su kawo sauki game da hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa al'ummar jihar.

Eata sanarwa da Kwamishinan rundunar, Ayuba N. Elkanah ya aike wa manema labarai ranar Lahadi ta jaddada matakin da gwamnan jihar Mohammed Bello Matawalle ya bayar da umarnin dauka domin shawo kan matsalar.

Mun zayyano matakan kamar yada Kwamishina ya bayyana:

  • An rufe dukkan kasuwannin da ke ci mako-mako a fadin jihar sai abin da hali ya yi.


  • An ha hana sayar da fetr a jarkoki


  • An hana zirga-zirgar babura da babur mai kafa uku wato Keke Napep a Gusau babban birnin jihar daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe, yayin da aka hana yin hakan a kananan hukumomin da ke wajen Gusau daga shida na dare zuwa shida na safe.


  • An hana dukkan gidajen mai sayar da fetur da ya wuce na naira dubu goma ga motocin haya.
  • An haramta daukar itace a dukkan fadin jihar.


  • An dakatar da daukar dabbobi a fitar da su daga jihar, sanna dole a gudanar da cikakken bincike kan dukkan dabbobin da za a shiga da su jihar.


  • An hana 'yan acaba daukar mutum fiye da biyu a lokaci daya


  • Kauyuka 9 a jihar Zamfara sun tara wa ƴan bindiga kuɗi


  • Zamfara Circle: Ƴan bindiga sun mamaye ƙauyuka 70 a Zamfara


  • Mahukunta sun yi amanar cewa gungun 'yan bindigar suna amfani da wadannan ayyukan tattalin arziki don kai hare -haren ga al'ummomi.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkanah, ya shaida wa manema labarai a Gusau babban birnin kasar, cewa an umarci hukumomin tsaro da su aiwatar da sabbin matakan da gwamnati ta sanar.

    Najeriya na fama da matsalar kashe-kashen mutane da ta yi muni da kuma yan bindigar da ke sace mutane don karbar kudin fansa .

    Ga dukan alamu hukumomi da iyalai da kuma al'umomi suna ɗaukar matakai don shawo kan matsalar.



    Read full article

    Source: BBC