BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Matsalar wuta: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin Najeriya

 124230739 09b93aa3 9028 4058 81ff A8b6e97f696d Najeriya na fama da matsalar wuntan lantiriki

Thu, 21 Apr 2022 Source: BBC

'Yan Najeriya sun sake tsintar kansu cikin yanayi na rashin wutar lanrtarki a wasu sassa kasar da dama, abin da ya sake jefa su cikin duhu da korafe-korafe kan yada rashin wutar baki daya ke shafarsu da sana'arsu.

A wannan lokaci mai kamar yada mahukuta ke cewa matsalar rashin wutar lantakin na da nasaba da faduwar babban layin lantarki na kasa a Najeriyar. Sai dai wannan shi ne karo na hudu da ake fuskantar wannan matsala a watani biyu jere.

A baya mahukuntan kasar sun danganta alamarin kan masu fasa bututun mai da ke jihar Bayelsa a yankin kudu maso kudancin kasar.

Babban layin wutar lantarkin ya dogara kacokan a kan iskar da ake samar masa daga bututun man na Bayelsa kuma a duk lokacin da aka samu matsala to hakan na kawo cikas wajan samar da wutar lantarki ga kasar baki daya.

Duk da cewa babu cikaken bayani a kan ko menene ya janyo faduwar wutar lantakin a wannan karon, ma'aikatar wutar lantaki ta kasar ta ce matsalar da aka samu a babban layin wutar lantarki na kasar a ranar 18 ga watan nan na Afrilu ta sa an kara samun raguwar wutar da ake da ita da megawat 903 daga cikin wanda ake da shi.

Sanarwar ta ce a ranar 17 ga watan Afrilu kasar ta rika samar da megawat dubu 3,829 amma a washegarin ranar ta ragu zuwa 2,926 saboda matsalar da ta samu.

Hakan ya janyo karancin wutar a fadin kasar kuma 'yan Najeriya da dama musaman masu harkokin kasuwanci sun koka a kan yadda yawan daukewar wutar lantarki ke kassara harkokin kasuwancinsu.

Wata mata mai sana'ar gyran gashi jiki a birnin Kano ta shaidawa BBC matsalar ta fi kamari ungwar da suke zama.

"A in da mu ke ba ma samun wuta kwata kwata, idan an samu ma sai cikin dare kuma a lokacin duk wani mai aiki ya kulle wurin aikin shi" in ji ta.

Shi ma wani mai sanar dinki ya ce a bana zai wuya su cika alkauran dinkin saboda yawan daukewar wutar lantakin.

"Aikin da ya kamata mu yi a cikin kashi 100, yanzu bai wuce mu iya yin kashi talatin ba ko kashi 20". In ji shi

A baya sai da shugaba Muhammadu Buhari ya ba 'yan Najeriya hakuri kan daukewar wutar lantarki inda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan gyra sai dai ga dukkan alamu matakan ba su soma tasiri ba



Read full article

Source: BBC
Related Articles: