BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Mino Raiola: Wakilin Pogba ya mutu na da shekara 54

 124373120 Nintchdbpict000323259536 Marigayi Raiola tare da Paul Pogba

Thu, 5 May 2022 Source: BBC

Babban menejan kwallon kafa da ya fito da manyan 'yan kwallo a duniya ya mutu yana da shekara 54 a duniya.

Dan kasar Netherlands da Italiyan na wakiltar manyan 'yan kwallo irinsu dan wasan gaban Borussia Dortmund Erling Haaland da na Manchester United Paul Pogba da kuma na AC Milan Zlatan Ibrahimovic.

Marigayin shi ne shugaban zauren kwallon kafa, da ke jagorantar gabatar da ejan da kuma 'yan wasansu.

"Za mu yi rashin shi har abada," in ji sanarwar da iyalansa suka fitar.

Ta ce "muna sanar da mutuwar babban eja da yake lura da wadanda yake wakilta cikin bakin ciki da jimami.

"Ya yi kokari kan 'yan wasan da yake wakilta har lokacin numfashinsa na karshe. Kamar ko yaushe Mino yana sanya mu alfahari bai taba watsa mana kasa a ido ba.

"Rayuwarsa ta sauya rayuwar mutane da yawa da kuma aikinsa ya bude wani sabon babi a fagen kwallon kafar zamani."

Sanarwar ta kara da ce "Burin Mino na ganin ya mayar da fagen kwallon kafa wuri na jin dadi ga 'yan wasa zai ci gaba da dorewa.

"Muna godiya ga kowa saboda nuna goyan bayan da aka nuna tare da tabbatar da darajar iyali da 'yan uwansa lokacin da aka shiga tashin hankali."

Raiola, ya wakilci dan wasan Belgium Romelu Lukaku da na Italiya Mario Balotelli da na Netherland de Ligt da dai sauransu.



Read full article

Source: BBC