BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Muslihu Yusuf Ali: Kansilan da ya dauki masu bayar da shawara 18 a Kano

Kano State Map Jihar Kano na Arewa maso yammacin Najeriya

Fri, 18 Jun 2021 Source: BBC

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:



Muslihu Yusuf Ali na daya daga cikin kansilolin karamar hukumar Kumbotso da ke Kano A Arewacin Najeriya kuma shi ne bulaliyar majalisar.

Sabanin yadda aka saba, Muslihu ya nada masu ba shi shawara har guda 18 domin tabbatar da cewa ya gudanar da aikinsa kamar yadda ya tsara tun ma kafin ya samu kujerar ta kansila.

Muslihu, wanda ya fara tsayawa takarar neman kansila a shekara 2007, ya kuma samu nasarar shiga majalisar kansilolin a 2021 bayan takara karo na biyar, ya ce “na debi masu bayar da shawar ne kasancewar an dade ana gwagwarmaya tare.”

Ya kara da cewa wasu “ ‘yan unguwarmu ne wasu kuma ma ban san su ba amma na dauke su saboda gogewarsu.”

Dangane kuma da albashin da yake biyan masu ba shi shawarar, Muslihu ya ce “ ai shi albashi sirri ne”.



Read full article

Source: BBC