Halin damuwar da harin Hamas ya jefa mutum 200 da ta yi garkuwa da su a bayyane yake ƙarara - sai dai ƙungiyar ta daɗe tana riƙe da wasu Isra'ilawa biyu tsawon shekaru.
Ba a san wasu bayanai da yawa ba game da ɗan Habasha mai shaidar zama ɗan Isra'ila Avera Mengistu da kuma Balarabe ɗan Isra'ila Hisham al-Sayed, waɗanda ta kama a 2014 da 2015.
'Yan uwan wasu sojojin Isra'ila biyu na cikin takaicin cewa har yanzu Hamas na riƙe da gawarsu a Gaza tun 2014. An kashe Hadar Goldin da Oron Shaul a yaƙin da aka gwabza tsakanin Hamas da Isra'ila a shekarar.
Hamas wadda ke samun goyon bayan Iran kuma ƙasashen Yamma suka kallo a matsayin ta 'yan ta'adda, ta taɓa neman fansa mai girma kafin ta saki 'yan Isra'ila da ta kama.
Aviram Shaul, ɗan uwan Oron, ya ce kusan shelara 10 ke nan amma ba su ji wani labari daga Hamas ba kan wurin da gawar Oron take, babu wata alamar dawowar Oron.
A 2014 ne sojoji suka ga hular kwanon Oron da kuma rigar kare harsashi cikin wata hanyar ƙarƙshin ƙasa a Gaza. Amma tun daga nan, Aviram ya faɗa wa BBC: "Ina ganin Isra'ila ta manta da su [matattun sojojin].
"Yanzu dama ta samu ta dawo da ɗan uwana, saboda yanzu muna maganar iyalai 200 da ke da 'yan uwan da aka riƙe a Gaza. Gwamnati ba ta yi wani ƙoƙari ba wajen ceto ɗan uwana, amma dai dole yanzu su ƙara ƙoƙari."
Bayan tattaunawar sirri a 2011, Isra'ila ta kuɓutar da soja Gilad Shalit - amma sai da ta saki Falasɗinawa 1,027 daga gidan yarinta.
Yanzu Isra'ila ta haƙiƙance sai ta ga bayan Hamas kuma hakan na jawo kashe-kashe da rushe-rushe a Gaza saboda hare-hare ta sama. Saboda haka duk wata yarjejeniyar musayar fursunoni za ta zo da wuya.
Yayin da adadin mutanen da ake kashewa a Gaza ke ƙara yawa, fushin Falasɗinaw ma na ƙaruwa.
"Yanzu ina ganin fansar ba da fursunonin Hamas za a biya ba - da wasu abubuwan daban za a biya," a cewar Hadas.
Ya jaddada cewa Isra'ila na da zaɓi da dama: a kai hari don kuɓutar da su idan an gano inda suke; amfani "da kuɗi" - kamar biyan kuɗi, ko kayan agaji; ko kuma "a ƙyale shugabannin Hamas su gudu daga Gaza, zuwa kamar Gaza".
Game da zaɓi na ƙarshe, ya ce "dole sai ka galabaitar da su, don su ji cewa dole su ƙulla yarjejeniyar idan suna so su tsira da rayuwarsu".
"Ina ganin akasarin mutanen na hannun Hamas, amma da yawa ba su hannunta. Ina da tabbas cewa Isra'ila na yin duk abin da za ta iya wajen ganowa da kuɓutar da su ta ƙarfin tsiya."
Ya ce "ko da an fara fafata yaƙi sosai a Gaza dole sai Isra'ila ta yi wata yarjejeniya kafin ta iya kuɓutar da su, za ta yi ƙoƙari sosai". "Muna mutunta rai kuma za mu iya biya don kuɓutar da shi."
Fararen hular Isra'ila biyu da aka kama a 2014 "ba garkuwa aka yi da su ba", in ji Hadas, "sun je Gaza ne kuma suna da ɗan taɓin hankali".
Hamas ta ce Avera Mengistu da Hisham al-Sayed sojoji ne, amma wasu takardun gwamnatin Isra'ila da ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch ta gani sun nuna cewa fararen hula ne da aka yafe musu aikin soja na hidimar ƙasa.
Tila Fenta ta jagoranci fafutikar sakin Avera, amma ta ce gwamnatin Isra'ila ta ba ta kunya - tana mai cewa maganar da ƙasashen duniya ke yi kan mutanen da ke hannu za ta taimaka.
"Ina ganin damar dawowar Avera ta ƙara yawa, amma fa ba ni da wani ƙwarin gwiwa," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
Ta danganta jan ƙafar da ake yi wajen dawo da Avera da Hisham da ƙabilun da suka fito da kuma wariyar launin fatar da ake nuna wa Yahudawan Habasha da Larabawan Isra'ila.
"Ina jin cewa Avera na cikin mutanen da al'umma ba su ƙauna sosai saboda launin fatarsa, da lalurar ƙwaƙwalwarsa, da kuma yadda ya taso a yankin talakawa na Ashkelon.
"Waɗannan abubuwan ne suka sa ba a kula da shi. Da a ce fari ne, ko kuma daga babban yanki, da haka ba ta faru ba. Na san yanzu ba lokacin faɗar abu ne maras kyauta a kan ƙasata ba, amma dole a faɗi gaskiya."
Wani matashin na Isra'ila, Jumaa Abu Ghanima, an ce ya tsallaka zuwa Gaza a 2016 kuma har yanzu ba a san inda yake ba. Balaraben Isra'ila ne kamar Hisham kuma ba mamaki yana hannun Hamas, amma babu tabbas.
Kafin su shiga Gaza ba bisa doka ba, Avera da Hisham sun sha ɓata, kuma an yi musu tiyatar ƙwaƙwalwa, a cewar Human Rights Watch.
A watan Janairu, Hamas ta fitar da bidiyon wani mutum yana magana da harshen Hiburu: "Ni ne wanda aka kama Avera Mengistu. Tsawon wane lokaci zan kasance a hannun abokaina?" Iyalansa sun tabbatar shi ne, kamar yadda masu neman sakinsa suka faɗa wa BBC.
Firaminista Netanyahu ya faɗa wa mahaifiyar Avera cewa gwamnati ta samu "tabbaci" cewa ɗanta yana nan da rai. Ya ce Isra'ila ba ta daina yunƙurin dawo da shi da sauran mutanenta gida ba".
A watan Yunin 2022, Hamas ta fitar da bidiyon Hisham al-Sayed a hannunta. Mahaifinsa Shaaban al-Sayed ya tabbatar cewa shi ne a bidiyon.
Abin da Hamas kawai ta ce shi ne lafiyar Hisham ta taɓarɓare - ba wani ƙarin bayani. Ana iya ganin sa a kwance sanye da na'urar nimfashi a kusa da wani katin shaidar da Isra'ila ta ba shi.
Tzur Goldin, ɗan uwan Hadar Goldin, ya ce ya kamata Isra'ila ta tsara yadda za ta hana Hamas yin garkuwa da mutane.
Kuɓutar da mutanen da Hamas ke riƙe da su zai yi wahala. "Tsaka mai wuyar da ake shiga ke nan duk lokacin da za a yi yarjejeniya da 'yan ta'adda," Hagai Hadas ya faɗa wa BBC. Akwai kuma sauran zaɓin da ka iya zama masu kyau ko akasin haka."
Read full article