BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

NFF ta nada Salisu Yusuf sabon kocin Super Eagles ta gida

 124154287 Mediaitem124154286 Salisu Yusuf, sabon kociyan Super Eagles

Sat, 16 Apr 2022 Source: BBC

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da nada Salisu Yusuf a matakin sabon kociyan Super Eagles ta gida da ke buga gasar CHAN.

Haka kuma zai ja ragamar tawagar matasan kasar ta 'yan kasa da sheka 23 da ke buga wasannin Olympics.

Yusuf ya taba jan ragamar Super Eagles B a gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasa da ke taka leda a gida a Morocco, inda Najeriya ta yi ta biyu a 2018.

Kamar yadda NFF ta sanar a shafinta a Intanet ranar Alhamis ta ce zai yi aiki tare da Kennedy Boboye da Fatai Osho da Abubakar Bala Mohammed da kuma Fidelis Ikechukwu a matakin mataimaka.

Shi kuwa Eboboritse zai yi aiki a matsayin mai tantance yadda wasa ke gudana wato Match Analyst, yayin da aka nada Ike Shorounmu da kuma Suleiman Shuaibu a matakin kociyan masu tsaron raga.

Haka kuma NFF ta ce nan gaba kadan za ta sanar da sabon kociyan babbar Super Eagles da zarar ta cimma yarjejjeni da shi, sannan ta gabatar da shi.

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta rusa masu horar da Super Eaglees karkashin jagorancin Augustine Eguavoen, bayan da ya kasa kai kasar gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a bana - Ghana ce ta yi nasara a kan Najeriya da ci 2-1, bayan da suka tashi 0-0 a Ghana.



Read full article

Source: BBC