BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Najeriya 1-1 Ghana: Dalilan da suka sa Ghana ta hana Najeriya gurbin kofin duniya

 123941956 Mediaitem123941955 Yan wasan kwallon Najeriya, Super Eagles

Tue, 29 Mar 2022 Source: BBC

Ghana Black Stars ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya, bayan da ta tashi 1-1 da Najeriya ranar Talata.

Minti 10 da fara wasa, Ghana ta ci kwallo ta hannun Thomas Partey daga baya Najeriya ta farke ta hannun William Ekong minti 12 tsakani.

Ranar Juma'a Super Eagles ta tashi ba ci a gidan Black Stars a Kumasi a wasan farko da suka kara a neman gurbin shiga gasar kofin duniya.

Wannan shi ne karo na hudu da Ghana za ta halarci kofin duniya, bayan 2006 da 2010 da 2014.

Ita kuwa Super Eagles ta kasa zuwa babbar gasar tamaula ta duniya karo na bakwai, bayan da ta je a 1994 da 1998 da 2002 da 2010 da 2014 da kuma 2018.

Cikin watan Nuwamba za a buga gasar kofin duniya a karon farko a Qatar a 2022.

Dalilan da Ghana ta yi nasara a kan Najeriya:

Dama wasa tsakanin Ghana da Najeriya karawa ce ta hamayya, amma Ghana ce kan gaba a yawan nasara, inda bayan wasa 58, Ghana ta ci 25, Najeriya ta yi nasara a 12 da canjaras 21.

Bayan da tawagar Super Eagles ta je Kumasi ta tashi 0-0 a wasan farko, 'yan wasan Najeriya na ganin cewar a karo na biyu za su doke Ghana, duk da cewar super Eaglees kan kasa cin karawa a gida, wadda tun daga 2019 ta ci biyu daga wasa tara da canjaras hudu da rashin nasara uku.

Ko da yake Ghana ta kasa yin nasara a fafatawa biyar da ta yi a dukkan wasannin da ta yi, wadda ta ci uku da canjaras biyu, tun bayan da ta yi nasara a kan Afirka ta Kudu 1-0 a watan Nuwamba.

'Yan wasan Najeriya ba su sa kuzarin lallai za su ci Ghana ba, sai suka dunga taka leda kamar ba a jikinsu ba, suka dunga kura-kuran raba kwallo a tsakaninsu.

Ba wani salo da suke da shi na cin kwallo illa dai a buga ta zuwa Osimhen a sama, wanda 'yan bayan Ghana, Amartey da Djiku suka hana shi sakat.

Salon da Najeriya ta taka a Abuja bai kara mata komai ba, akwai tazara a koda yaushe tsakanin masu tsaron bayan Nageriya da masu buga tsakiya da masu cin kwallo.

'Yan wasan Super Eagles ba su da wani salo ko tanadi da za su ci Ghana, kowanne dan wasa da salon da ya buga a fafatawar.

Kocin Najeriya ya tabka kuskure, wajen zabar 'yan wasan farko 11 da suka buga masa fafatawar, sannan canji da ya yi bai yi masa wani amfani ba, tun da sunj kasa cin kwallo.

Duk da fitattun 'yan wasa da Super Eagles take da su ta kasa cin kwallo da farko sai da Ghana ta zura mata a raga, sannan ta farke a bugun fenariti.

Ba fahimtar juna tsakanin mai tsaron baya Ekong da Balogun, sannan mai tsaron raga, Uzoho ya kasa kwantar da hankali, tun bayan da kwallo ya shiga ragarsa.

'Yan wasan Najeriya da na Ghana da suka buga fafatawar:

  • F Uzoho


  • Ola Aina


  • W Troost-Ekong


  • L Balogun


  • C Bassey


  • F Onyeka


  • Peter Etebo


  • J Aribo


  • V Osimhen


  • A Lookman


  • E Dennis
  • Masu zaman benci

  • J Noble


  • D Akpeyi


  • Z Sanusi


  • (45) A Shehu


  • S Ajayi


  • K Omeruo


  • A Amoo


  • A Musa


  • K Iheanacho


  • M Simon


  • S Umar


  • O Ighalo


  • Tawagar Ghana

  • Jojo Wollacott


  • D Odoi


  • G Mensah


  • D Amartey


  • A Djiku


  • T Partey


  • M Kudus


  • I Baba


  • F Issahaku


  • J Ayew


  • F Afena-Gyan


  • Masu zaman benci

  • R Ofori


  • L Ati
  • A Yiadom


  • J Aidoo


  • D Kyereh


  • E Owusu


  • Y Yeboah


  • O Bukari


  • J Paintsil


  • K Wriedt


  • C Antwi-Adjej


  • Alkalin wasa: Sadok Selmi



    Read full article
    Source: BBC
    Related Articles: