BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Najeriya: Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP

 124192019 E529e461 7257 40ab 9b77 9217e64e95b4 Was kwamandojin ISWAP

Sun, 17 Apr 2022 Source: BBC

Rundunar sojin Najeriya ta ce jiragenta na yaki sun kashe shugabannin kungiyar masu tayar da kayar baya ta ISWAP akalla biyar a arewa maso gabashin kasar kusa da Tafkin Chadi.

Rundunar sojin sama ta kasar ta ce an kai harin ne tare da hadin gwiwar sojin sama na Nijar a kan wani sansanin mayakan na ISWAP yayin da suka taru domin wani aikin horo.

Baya ga kwamandojin mayakan da aka kashe, an kuma kashe 'yan kungiyar kusan saba'in a harin na ranar Alhamis din data wuce.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya, Air commodore Edward Gabkwet, ya shaida wa BBC cewa, sai da suka tabbatar masu tayar da kayar bayan sun taru a wajen, sannan aka je aka bude musu wuta.

Jami'in sojan ya ce da hadin gwiwar sojin saman Nijar aka kai harin, kuma dabarun da suka bi wajen kai harin, sun yi matukar tasiri da ma'ana.

Ya ce bayanan sirri sun nuna cewa an kashe mayakan na ISWAP kusan 70, baya ga lalata wuraren da suke ajiye kayan yaƙinsu da kuma baburansu na hawa.

Air commodore Edward Gabkwet, ya ce suna sane da irin abubuwan da ke faruwa da yankin arewa maso yammacin Najeriya, don haka ba za su gajiya ba har sai sun mukushe su.

''Za mu tabbatar da cewa mun kawar da su a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sannan za kuma mu tabbatar ba su samu wurin zama a arewa maso yamma ba, shi yasa muke cewa 'yan Najeriya su ba mu lokaci, ba zamu bar kowa ya hana su zaman lafiya ba" Inji Gakwet.

<>Karin bayani

Ba wannan ne karon farko da sojojin Najeriya suka kashe mayakan ISWAP ba, ko a watan Maris din 2022, sai da rahotanni suka ce mai yiwuwa an kashe jagoran kungiyar ISWAP na yankin yammacin Afirka, Sani Shuwaram da wasu mayakan kungiyar sanadin wani hari ta sama a yankin Marte na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Haka ma a watan Janairun 2022, jiragen yakin sojojin Najeriya sun kaddamar da hare-hare da dama kan maboyar mayakan kungiyar ISWAP din da ke a arewa maso gabashin kasar.

Inda bayanai suka tabbatar an kashe kwamandojin kungiyar ta ISWAP a Kirta Wulgo da ke jihar Borno a wannan makon.

Haka ma a shekarar 2021 sai da sabon jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya na Super Tucano ya tarwatsa mayaƙan ISWAP tare da lalata motocinsu na igwa a Gajiram da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Najeriya dai na fama da matsalar tsaro, kama daga hare-haren 'yan Boko Haram da ma na 'yan fashin daji da ke satar mutane don neman kudin fansa.

A ko da yaushe dai jami'an tsaro kan ce suna murkushe duk wasu masu tayar da kayar baya, amma kuma 'yan kasar na disa alamar tambaya a kan sahihancin hakan.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: