BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Olivier Giroud: Dan wasan Chelsea ya kammala zuwa AC Milan

Giroud Hatrick Olivier Giroud ya koma AC Milan daga Chelsea

Mon, 19 Jul 2021 Source: BBC

Dan wasan Chelsea, Olivier Giroud ya kammala komawa AC Milan, bayan kaka uku da ya yi a Stamford Bridge.

Dan kwallon tawagar Faransa, wanda ba a fayyace kan nawa ya koma Italiya ba, ya je Chelsea kan fam milyan 18 a Janairun 2018.

Mai shekara 34 ya ci kwallo 11 a wasa 31 da ya buga wa Chelsea a kakar da ta wuce har da karawa takwas a Premier League da aka fara wasa da shi a fili.

An rage sa Giroud a wasanni ne a kakar 2020-21, bayan da Chelsea ta dauki Kai Havertz da kuma Timo Werner a bara.

Dan wasan ya ci kwallo 39 a karawa 119 da ya yi wa Chelsea, wanda ya lashe Champions League da Europa League da kuma FA Cup.

Wanda ya lashe kofin duniya da Faransa ya buga wa tawagar wasan da Switzerland ta fitar da Faransa a zagaye na biyu a Euro 2020 a bana.

Haka kuma Giroud ya lashe FA Cup uku a Arsenal.

AC Milan ta yi ta biyu da tazarar maki 12 a teburin Serie A da Inter Milan ta lashe kofin kofin kakar da aka kammala.



Read full article

Source: BBC