BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Osinbajo zai kaddamar da takarar shugabancin Najeriya

 124113130 4a843b0e Aeb9 4913 A055 B5e89e72633e Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo

Mon, 11 Apr 2022 Source: BBC

A ranar Litinin din nan ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

A cewar wasu majiyoyi na shirin kaddamar da takarar sun ce ba wani taro na musamman za a yi wajen kaddamar da takarar ba.

Illa kawai za a fitar da wani hoton bidiyo wanda zai yi jawabi a kan burinsa na gadar Shugaba Muhammadu Buhari.

Za a sanya bidiyon a dukkan kafofin intanet, daga nan kuma sai 'yan kwamitin yakin neman zabensa su fara yakin gadan-gadan.

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da jawabi ga wani taron jama'a inda ya kaddamar da manufarsa ta tsayawa takara kamar yadda tsohon gwamnan jihar Rivers, kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ya yi a Fatakwal a ranar Alhamis din da ta wuce.

Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Ebonyi David Umahi, su sun yi bayani ne ga 'yan jarida a lokacin kaddamar da takarar tasu, bayan sun gana daban-daban da Shugaba Buhari.

Rahotanni sun ce kafin sakin bidiyon da za a yi a ranar Litinin, sai da Mr Osinbajo, ya yi buda baki tare da gwamnonin jam'iyyar APC a gidansa.

Tuni dai Osinbajo ya bude ofishin kamfen dinsa a Wuse da ke Abuja.

Baya ga kewayawa da zai yi jihohi domin neman goyan baya, 'yan kwamitin yakin neman zaben nasa za su shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023.

A daya daga cikin tambayoyin da ke cikin wannan kuri'a ta jin ra'ayi, an tambayi jama'a kan su zabi wanda suka ga ya fi dacewa da shugaban kasa tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da Tinubu da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Ana ganin Farfesa Osinbajo, zai samu magoya baya, amma yadda zai bullo a siyasance ya kalubalanci manyan masu sha'awar takarar biyu Mr Tinubu da Mr Amaechi, shi ne abin jira a gani.



Read full article

Source: BBC