BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ra’ayi: Salon dora alhakin da kasar Algeria ke yi ya bankado gagarumin rikicin siyasa

 120363259 Mediaitem120343724 An sake komawa zanga-zanga a Algeria cikin wannan shekarar don neman a kawo sauye-sauyen siyasa

Fri, 3 Sep 2021 Source: BBC

Muddin sunan kasa a hukumance na da kalmomi kamar "dimokaradiyya" da kuma "shahara", akwai jayayyar cewa babu ko daya daga cikinsu.

Ka dauki misalin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Mutanen Korea da aka fi sani da Korea Ta Arewa wacce daukacinta kasa ce mai jam'iya daya.

Sai kuma Algeria, wacce sunanta a hukumance ya yi iri daya da Korea Ta Arewa - Jamhuriyar Dimokaradiyyar Mutanen Algeria.

Duk da cewa ba ta kai matsayi kamar na Pyongyang ba, ka tambayi duk wani daga cikin dubban mutanen da suka taba fita kan tituna a Algeria tun a shekaar 2019, kuma za ka ji ra'ayoyinsu sun zama daya a kan cewa kasarsu ba mai bin tafarkin dimokaradiyya ba ce, ba kuma shahararriya ba ce.

Za su fada maka cewa gwamnatin kasarsu ta shafe shekaru da dama a karkashin mulkin wasu 'yan tsiraru, inda sojoji ne suke rike da madafun iko a fakaice da sunan mulkin farar hula, kana suna amfani da arzikin man kasar suna cika aljihunsu.

Har wa yau, masu zanga-zangar na kallon zabukan 'yan majalisu da na shugaban kasa a matsayin yaudara don a nuna halascin gwamnati wanda kuma ba ta da shi.

Wani abu karara game da "Jamhuriyar Dimokaradiyyar mutane" shi ne a lokutan rigingimun kasa, martanin gwamnati na farko kan kasance ne a dora laifi a kan baki 'yan kasashen waje ko kuma "masu yi wa gwamnati zagon kasa".

Lokacin da kasar Algeria ta fuskanci bala'in gobarar daji a watan da ya gabata wacce ta lalata dubban kadadar bishiyoyi da shuke-shuke tare da hallaka akalla mutane 90 da suka hada da wasu sojoji 30 da aka aike domin aikin kashe gobarar, martanin farko da ya fito daga gwamnati shi ne dora laifi a kan masu aikata kone-kone, tare da lasar takobin farauto su.

Ba kuma da samar da wata shaida ba. Babu wata kalma guda daya game da sauyin yanayi ko kuma cewa akwai irin wannan wutar dajin da ke ci a fadin kasashen yankin Mediterranean.

Martani iri daya ne a lokacin da wasu bayanai na abin damuwa da suka faru na hallaka tare da kone gawar Djamel Ben Ismail mai shekaru 37, wanda ya je yankin Kabylie don taimaka wa 'yan kasarsa ta Algeria kashe wutar.

An dauki faifen bidiyon a wayar salula kana aka rika yadawa a ko ina a shafukan sada zumunta. 'Yan kasar ta Algeria sun kadu matuka game da abin da suka bayyana dabbancin wadanda suka aikata ta'asar.

Babban abin kunya ga gwamnati, lamarin ya faru a kan idanun 'yan sanda wadanda ba su tabuka komai ba wajen hana tafka wannan ta'asa.

Gwamnati ta kare jami'an, tana mai cewa wasu gungun mutane ne suka kai musu hari, suka fisge Isma'il daga cikin motar 'yan sandan.

Mahukunta sun kama gwamman mutane - na baya-bayan nan sun kai kusan 80 - kana ta zarge su da hannu a kan aikata laifin.

Kamar kuma yadda aka saba, an nuna su a kafar talabijin daure da ankwa a hannu a yayin da suke ikirari, wanda ya daidai da muradun gwamnati na dora alhaki a kan wata kungiyar siyasar da ba ta dade da ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ba.

Kungiyar, wacce aka fi sani a takaice da MAK, na fafutikar neman 'yancin cin gashin kan Kabylie, wani yanki da 'yan kabilar Berber suka fi yawa a arewacin kasar ta Algeria, inda ta fi fama da abkuwar wutar daji.

Yankin kuma nan ne asalin 'yan kungiyar Hirak - kungiyar da zanga-zangarta ta haifar da kawo karshen mulkin shekaru 20 na Shugaba Abdelaziz Bouteflika a shekarar 2019.

Hirak ta cigaba da kalubalantar tsoffin aminan Bouteflika da suka gaje shi.

Abubuwan da ke daure kai game da kisan kan

Wani abu da aka saba gani game da "Jamhuriyar Dimokaradiyyar mutanen" shi ne cewa yana da matukar wahala mutane su yarda da abubuwan da kafafen yada labaran kasar ke yadawa.

Hakan ya sa aka yi ta shaci-fadi game da ainihin ko su wane ne ke da alhakin wannan mummunan kisa na Isma'il.

Balarabe ne shi, wadanda suka hallaka shi matasan kabilar Berber ne.

Laabari daya da ya shahara a shafukan sada zumunta da kuma a tsakanin 'yan asalin kasar ta Algeria da suka nemi mafaka a kasashen waje yan una cewa kisan da alamu wani yunkuri ne na jami'an tsaron farin kaya - na ruwa wutar rikicin kabilanci, tare da kartakar ta hankulan fushin jama'a kan gazawar gwamnati.

Wasu sun cika da mamaki kan ko an yi amfani da Ismail ne a matsayin wata hanyar cimma burin gwamnati na haddasa fitina a yankin Kabylie, don ta nuna tabbatar wa da jama'a gaskiyarta na tsauraran matakan da ta ke dauka a kan masu adawa da ita.

Yanzu gwamnati ta sanar da cewa za ta biya diyya ga duk wadanda bala'in wutar dajin ta shafa.

Game da batun kisan Mista Ismail, 'yansanda sun ce an gano wayar salularsa dauke da "bayanai masu daga hankali game da ainihin dalilan da suka haddasa kisan shi".

Amma kuma, wadannan ba za a iya bayyana su ba saboda binciken da ake kan gudanarwa.

'Dora alhaki a kan kasar Morocco'

Bayan shawo kan "barazanar cikin gida", gwamnati ta kara kaimi kan dora alhakin da ta ke yi wajen sanar da cewa makwabciyarta, kuma tsohuwar abokiyar gogayyarta a yankin, kasar Morocco - an same ta da rura wutar rikici ga kasar Algeria.

Ta yanke huddar difilomasiyya da Rabat kana ta sanar da cewa ba za ta sake bai wa kasar ta Morocco iskar gas ta Algeria ba, da aka kididdige a yawanta ya kai kafa miliyan 800 a ko wace shekara.

Kasar Morocco ta yi watsi da zarge-zargen kasar ta Algeria kana ta bayyana fatan cewa nan ba da jimawa ba za a sake kulla dangantakar difilomasiyya.

Amma har yanzu ba ta bayyana komai ba kan yiwuwar irin tasirin da matakin kan bukatunta na makamashi ba.

Masu sun yi nuni da cewa dora alhaki kan kasar Morocco da kuma kungiyoyin siyasa na cikin gida wata tsohuwar dabara ce ta karkatar da hankula daga jama'a kan gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalolin cikin gidan kamar su abkuwar wutar daji, da annobar korona da kuma rashin aikin yi.

A watan da ya gabata, yayin da cutar korona ta kara bazuwa cikin yanayi na karancin iskar shaka ta oxyegen ga wadanda cutar da yi wa tsanani, gwamnati ta bayar da umarni ga kafafen yada labarai da kada su "'yada labarai marasa dadi".

Amma duk a haka, a zahiri, annobar ta bai wa gwamnati damar dakatar da zanga-zangar da kungiyar Hirak ta shirya. Wani yunkuri ne mai kyau da ta fake da batun lafiyar al'umma wajen hana taruwar jama'a da kuma gangami.

Nuna fushi a kan sojoji

Suna son rushe daukacin tsohuwar dokar kana su yi watsi da abin da suka kira sake hada tsofaffin kujeru.

Irin kallon da suke yi wa Shugaba Abdelmadjid Tebboune kenan, wanda aka zaba a shekarar 2019.

Taken shi ne: "Dole ne dukkaninsu su yi murabus" - kana akwai sojoji a tare da su.

Sun ware wani babban jami'in soja daya Janar Saïd Chengriha, suna mai amannar cewa shi ne shugaban kasa na zahiri.

Bacin ran su na da tushe a cikin gazawar gwamnati wajen samar da 'yancin walwalar siyasa da kuma jin dadin jama'a.

Gwamnati ce wacce ta gina halaccinta a kan abubuwan da suka shafi labaran nuna kin jinin mulkin mallaka, wanda ba shi da tagomashi a yanzu a tsakanin al'ummar matasa, akasari da aka haifa bayan samun 'yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1962.

Tambayar yanzu ita ce, shin sabuwar kungiyar Hirak za ta iya cimma abubuwan da a baya suka sanyaya gwuiwar sauran zanga-zangar kungiyoyi a akasarin yankin Afirka ta Arewa da kuma Gabas ta Tsakiya - 'yanci da kuma bin doka da oda?



Read full article

Source: BBC