BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Real Betis vs Real Madrid: 'Yan Real Madrid da suka je Betis buga La Liga

 120317450 Benzema2 Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid

Sun, 29 Aug 2021 Source: BBC

Real Madrid ta ziyarci Real Betis domin buga wasan mako na uku a gasar La Liga da za su kara ranar Asabar.

Za su kara ne a filin wasa da ke Benito VillamarĂ­n, kuma wasa na uku da Real za ta yi a waje, bayan Alaves da Levante.

Real ta fara cin Alaves 4-1 a wasan makon farko da bude La Liga ta bana, sannan ta tashi 3-3 a gidan Alaves a makon jiya.

Real Madrid ta doke Betis har gida da ci 3-2 a bara ranar 26 ga watan Satumbar 2020, sai dai sun tashi 0-0 a gidan Real ranar 24 ga watan Afirilun 2021 a fafatawar La Liga gida da waje.

'Yan wasan da Carlo Ancelotti ya je da su Betis:

Masu tsaron raga: Courtois da Luis Lopez da kuma Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Alaba da Vallejo da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Casemiro da Valverde da Lucas V. da Isco da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Jovic da Bale da Vini Jr. da kuma Rodrygo.



Read full article

Source: BBC