BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Rikita-rikitar komawar Gwamnan Zamfara Mutawale zuwa APC

 112392054 Zamf1 Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle

Tue, 29 Jun 2021 Source: BBC

Ana ci gaba da muhawara kan sauyin sheƙar da Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle zai yi nan gaba zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

An shafe tsawon lokaci ana yaɗa jita-jitar cewa gwamnan yana shinshina jam'iyya mai mulki kafin APCn ta tabbatar da komawarsa a ƙarshen mako.

Sai dai a iya cewa yayin da APC ta shirya gagarumar tarba kan wannan ƙaruwa da ta samu, sauyin sheƙar ga alama ya tada ƙura mai girman da ba san lokacin lafawar ta ba a nan gaba.

Rahotanni masu ƙarfi na cewa a ranar Talatan nan ne ake sa ran gwamnan zai sauya sheƙa daga jam'iyyar siyasa ta PDP zuwa ta APC.

Martanin jam'iyyar PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, wato PDP ta ce har yanzu da wai-wai take ji batun sauyin-sheƙar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Ta ce tana ci gaba da jira har sai gwamnan ya shelanta fita daga PDP, kafin ta ambata matakin da za ta ɗauka.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri shi ne sakataren jam'iyyar na ƙasa, kuma ya ce maganar ta girgiza su, kuma ba za su zuba ido a kan batun ba.

"Babu shakka abin ya dami jam'iyyar PDP. babu jam'iyyar siyasa da za ta rasa gwamna mai ci a ce bai dme ta ba." Amma tun da abu ne da dole sai an yi, to za mu ga irin matakan da za mu dauka bayan gwamnan ya koma jam'iyyar ta APC.

Sanata Tsauri ya ce a hukumance, jam'iyyarsu ta PDP tana daukar labarin a matsayin jita-jita ne domin gwamnan bai fito fili ya sanar da cewa zai yi ƙaura daga PDP ba.

Sai dai da alama jam'iyar ta PDP za ta kalubalanci matakin gwamnan da zarar ya sauya sheƙa, domin tana kallon matakin gwamna Mutawalle tamkar ta taka doka, ganin yadda aka tafka shari'a kafin kotu ta tabbatar wa jam'iyyar ta PDP mukamin.

Sanata Tsauri: Idan ta tabbata ya bari, to mu kuma za mu ɗauki mataki, domin kotun kolin Najeriya cewa ta yi kujerar gwamnan Zamfara ta PDP ce ba ta Muhammadu Bello Mutawalle ba.

Sai dai wannan halayyar ta zama ruwan dare gama duniya a siyasar Najeriya, domin ita ma jam'iyyar ta PDP ta ci gajiyar sauya sheka a baya.

Misali, gwamnan Binuwai Samuel Ortom da na Edo Godwin Obaseki duka sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a cikin wa'adin wannan gwamnatin.

Sai dai yayin da jam'iyyarta PDP ke murza kambu, rahotanni daga Gusau, babban birnin na jihar Zamfara na cewa ana can ana ta shirin wani gagarumin bikin tarbar gwamna Mutawallen daga PDP zuwa APC.

Kuma ana sa ran gwamnan zai sauya sheka ne da magoya dubban bayansa, ko da yake akwai wadanda ba za su bi shi ba.

Cikin wadanda ba za bi gwamnan ba, akwai dan majalisar tarayya daga jihar, Kabiru Yahaya Classiq.

"Na zabi in tsaya ne a PDP bisa ga alkawarin da na dauka tsakanina da Allah. babu dalilin da Allah zai ba ni nasara a nan, sai in dauki ba zai ba ni wata nasara ba sai in na koma can."



Read full article

Source: BBC