BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ruben Dias: Zai ci gaba da wasa a Manchester City zuwa karshen 2027

 120329956 Dias Mai tsaron bayan Manchester City, Ruben Dias

Mon, 30 Aug 2021 Source: BBC

Mai tsaron bayan Manchester City, Ruben Dias ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Etihad zuwa karshen 2027.

Dan kwallon tawagar Portugal, mai shekara 24 ya koma City da taka leda kan kwantiragin kaka shida a Satumbar 2020 kan fam miliyan 65.

Ya bayar da gudunmuwar da City ta ci Premier League da Carabao Cup da kai wa wasan karshe a Champions League a bara.

Dias shine ya lashe kyautar dan wasan da ba kamarsa da kungiyar marubuta labarin wasanni da ' kungiyar 'yan kwallon Premier League ta karrama a kakar da ta wuce.

Dan kasar Portugal ya buga wa City karawa 50, kuma shine ya lashe kyautar mai tsaron baya da ba kamarsa a Champions League a 2020-21.

Ranar Asabar 28 ga watan Agusta, City ta doke Arsenal 5-0 a wasan mako na uku a gasar Premier League a Etihad.



Read full article

Source: BBC