BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Shawarwari 10 da gwamnonin Kudu suka yanke kan makomar Najeriya

 119252504 Mediaitem119252503 Gwamnonin kudancin Najeriya sun taru ne a Legas

Wed, 7 Jul 2021 Source: BBC

Ƙungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta yanke shawara kan matakai daban-daban game da makomar ƙasar a taron da ta gudanar ranar Litinin a birnin Lagos.

A sanarwar da gwamnonin suka fitar, wadda shugabansu Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanya wa hannu, sun bayyana goyon bayansu ga kasancewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.

Sun gudanar da taron ne kwanaki kaɗan bayan jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun kai sumame gidan mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawan nan Sunday Igboho, inda suka gano manya-manyan makamai.

Hakan na faruwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta kamo Mr Nnamdi Kanu, mai rajin ɓallewa daga ƙasar domin kafar ƙasar Biafra.

Wasu na ganin gwagwarmayar da mutanen biyu suke yi tana da nasaba da siyasa kodayake gwamnonin sun yaba kan matakin da gwamnatin tarayya take ɗauka domin wanzar da tsaron a yankin.

Ga matakan da gwamnonin suka ɗauka game da makomar Najeriya:

  • Sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci

  • Gwamnonin kuma sun amince da wasu buƙatu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur.


  • Sun sake jaddada goyon baya ga haɗin kan Najeriya.


  • Tabbatar da bukatar ƴan sandan jiha


  • Dole ne duk wata hukumar tsaro ta nemi izininsu kafin ƙaddamar da samame a jihohinsu


  • Ƙungiyar gwamnonin ta koka kan yadda a cewarta ake nuna son kai wajen tabbatar da adalci a Najeriya tana mai cewa ya kamata duk wanda za a kama a bi doron doka da 'yancin ɗan ƙasa


  • Sun tsayar da ranar 1 ga Satumban 2021 da dokar hana kiwo za ta fara aiki a dukkanin jihohin kudanci
  • Ta yanke shawarar cewa dole a raba kuɗin da ake cirewa daga Asusun Tarayya na Gidauniyar 'yan sanda ta ƙasa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi


  • Ƙungiyar gwamnonin ta yi fatali da matakin da majalisar dokokin ƙasar ta suka ɗauka na cire aika sakamakon zabe ta hanyar intanet daga dokokin zaben kasar;


  • Kungiyar kuma ta zaɓi Lagos a matsayin hedikwatar ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya




Read full article
Source: BBC