BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Shin cin fatar naman kaza yana da amfani?

C5992750 29ed 11ed 91e8 453e424fc8c9 Hoton alama

Mon, 19 Sep 2022 Source: BBC

Nama kaza abin so ne a duniya. Shi ne naman da mutane suka fi ci fiye da kowane nau'in nama a duniya.

Hukumar kula da harkokin noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa mutane sun ci akalla tan miliyan 133 na tsokar kaza a duniya cikin 2021. Cin naman kaza abu ne gama-gari saboda yana da araha kuma ba shi da alaƙa da wani addini ko al'ada, yana kuma cike da sinadaran protein da vitamin.

Naman kazar yana ƙara wa mutane lafiyar zuciya sai dai akwai jita-jita da ake yaɗawa game da cin tsokar kaza. Misali, fatar naman kaza na ɗauke da kashi 32 cikin 100 na kitse - abin da ke nufin duk lokacin da muka ci fatar naman kaza mai nauyin kilo 100 , yana ɗauke da kitse mai nauyin gram 32, in ji María Dolores Fernández Pazos, wata masaniya kan abinci mai gina jiki a cibiyar CINCAP da ke Argentina.

Daga cikin kitsen naman kaza, a bayaninta, yana ɗauke da kitse mara illa da ke inganta mizanin cholestorol a cikin jini. Sannan kashi uku na kitsen ɗaya daga cikin kitse mai illa na ba da gudummawar ƙara mizanin cholestorol mara alfanu.

Wannan mizani ne iri ɗaya da ke jikin tsokar kaza. A don haka, masaniyar ta bayyana cewa "idan muka ci naman kaza tare da fatar, muna ƙara yawon sinadaran calories a duk lokacin da aka ci naman da kashi 50 cikin 100.

"Idan a misali muka ci naman ƙirjin kaza mara fata hakan na nufin muna laƙume sinadaran calories 284 (a cewar Sashen lura da harkokin noma da abinci mai gina jiki, kashi 80 cikin 100 na sinadaran calories daga sinadaran protein da kashi 20 cikin 100 daga kitse.

Amma ƙididdigar ta ƙaru sosai idan ba a haɗa da fatar ba, naman ƙirjin kaza na da kashi 386 calories sannan an samu kashi 50 daga kitse. Wannan ne dalilin da ya sa a cewar masaniya kan abinci mai gina jiki, Dolores Fernandez, taba da shawarar cire fatar naman kaza kafin a ci, don kar mutum ya ƙara wa abincin da yake ci kitse".

Shin yana da kyau a sake daskarar da naman kazar da aka daskarar?

"A'a. Bai kamata a sake daskarar da naman kazar da aka daskarar ba,'' a cewar wani masani kan harkar abinci mai gina jiki. ''Dalilin da ya sa ake saka abinci a cikin firinji shi ne domin hana wasu kwayoyi shiga abincin.

Don haka, idan aka sake sanya abinci a cikin firinji, wasu ƙwayoyi za su shiga ciki. ''Wannan kuma ya shafi dukkan naman da aka daskarar. Hanyar da ta dace na daskarar da abinci shi ne idan aka dafa shi.

"Ta wannan hanyar tare da dafa shi yadda ya kamata, za mu taƙaita shigar ƙwayoyi wadda zai ba mu damar daskarar da naman, a cewar Dolores Fernandez.

Wace hanya ce ta fi dacewa a daskarar da naman kaza?

A cewar mutane, hanyar da tafi dacewa na daskarar da naman kaza ita ce sanya ta cikin firinji. “Idan aka daskarar da shi a ɗakin da akwai alamun zafi, ƙwayoyi za su iya shiga da kuma za su ɓata naman”.

Firinji ba zai daskarar da naman kaza da wuri ba inda zai iya ɗaukar sa'a 24 don daskarar da kaza guda ɗaya.

Lokacin da yafi dacewa na cire kazar daga firinji ita ce lokacin da ta gama daskarewa.

Masana sun ce kaza ba za ta iya daskarewa ba a ɗaki mai zafi ko kuma cikin ruwa mai zafi.

Abin da ya sa shi ne wasu wuraren ajiya, na sayar da kaji masu launi daban-daban, inda na wasu yafi na wasu kyawu. Launin naman kaji kan bambanta musamman ma duba da irin abincin da aka rika basu, a cewar masana.

Yadda za a kaucewa naman kaza mai guba

Kaza na ɗaya daga cikin dangin abinci da aka fi ci a duniya, sai dai sau tari, nama na cikin abinci da ake samun guba. Ana samun ƙwayoyin cututtuka cikin naman da ba a dafa ba.

Wannan ne ya sa mutane kan hadu da abinci mai guba idan basu dafa kaza yadda ya kamata ba ko kuma abincin da ya ɓaci suka kuma haɗa da kayan sha.

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta Amurka, CDC, ta ƙiyasta cewa akalla mutane miliyan ɗaya ke kwantawa rashin lafiya a ƙasar duk shekara bayan cin nama mai guba.

Masana sun bayar da shawarwari ga mutane na yadda za su kaucewa cin nama mai guba: masana sun ce mutane su riKa wanke hannunsu kafin dafa kowane irin abinci, musamman lokacin rike nama kafin dafa shi.

Masana sun kuma ce mutane su rika amfani da kayan dafa abinci masu tsafta domin kare abincinsu daga lalacewa.



Read full article

Source: BBC