BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Sunday Igboho: Sarakunan gargajiya na son jagoran yan awaren Yarbawa ya mika wuya

 119365649  116858475 131119800 142834210932944 8803371593278584988 O Sunday Igboho

Tue, 13 Jul 2021 Source: BBC

Wasu sarakunan gargajiya na Yarbawa a kudu maso yammacin Najeriya sun ce dole ne Sunday Adeyemi, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya mika kansa ga hukumar DSS.

Sunday Igboho dai ya kasance wani da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ke nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da adana bindigogi domin tayar da zaune tsaye a yankin Yarbawa.

Sai dai tuni Sunday Igboho ya musanta adana makamai a gidansa.

Tun farko Igboho ya zargi sarakunan gargajiyar da karbar na goro a hannun hukumomi domin ganin an kama shi da kuma ganin bayansa.

Amma Basarake Ahmed Adekunle Makama Oluwa, mai daraja ta daya a jihar Osun, ya musanta wannan iƙirari na Igboho inda ya ce kamata ya yi jagoran yan awaren ya mika kansa a mutunce kuma cikin dadin rai.

"Kamata ya yi ya mika kansa ga hukumar tsaro, hukumar leken asiri ta kasa DSS watakil ya samu sassauci amma idan ya jira, ko ya je buya, komai dadewa sai an same shi". in ji Basaraken.

Shi ma Olubadan na Ibadan Oba Salihu Adetunji ya musanta zargin karbar kudi a hannun gwamnatin ƙasar domin kamun Sunday Igboho ya yiwu.

Sunday Igboho dai ya bukaci a biya sa ta'adin da aka yi masa cikin gidansa abin da Basarake Hamed Adekunle Oluwa yake ganin batun hakan bai taso ba.

A cewarsa, idan za a biya Sunday Igboho, toh za a yi maganar biyan su Muhammad Yusuf da Abubakar Shekau na Kungiyar Boko Haram.

Wasu jama'a a yankin na Kudu maso yammacin Najeriya na yi wa Sunday Igboho kallon mai fafutukar tabbatar da yancin Yarbawa.



Read full article

Source: BBC