BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

TV

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas

C7e171d0 7351 11ee A503 4588075e3427 António Guterres, babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Isra'ila ta mayar da martani da kakkausar murya kan kalaman da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi game da yaƙin Gaza a lokacin taron kwamitin tsaro na majalisar.

António Guterres ya ce ya yi alla-wadai ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba, da munanan hare-haren da 'yan bindigar Hamas suka kai Isra'ila mako biyu da ya wuce, sai dai abu ne mai muhimmanci a yarda cewa hare-haren "ba haka kawai suka faru ba".

To amma jakadan Isra'ila a Majalisar, Gilad Erdan ya zarge shi da ƙoƙarin ''kare ta'addanci'', inda ya buƙace shi ya gaggauta yin murabus.

Daga baya kuma ya ce Isra'ila za ta janye bizar ƙasarta daga hannun jami'an Majalisar Dinkin Duniyar.

Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya yi watsi da kiran tsagaita wuta a wani mataki na martanin da ƙasarsa ke ɗauka kan hare-haren Hamas, waɗanda suka kashe aƙalla mutum 1,400, tare da yin garkuwa da mutum 222.

Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce fiye da mutum 6,500 aka kashe a yankin tun bayan da Isar'ila ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya da makaman atilare, yayin da dubban dakaru suka taru a ƙasa da nufin mamayar yankin.

Yayin da yake jawabi ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York ranar Talata, Mista Guterres ya ce yanyin da ake ciki a gabas ta tsakiya na ci gaba da taɓarɓarewa a kowacce sa'a.

Sannan ya yi kira ga duka ɓangarorin su martaba tare da kare fararen hula.

"Na yi alla-wadai ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba game da mummunan harin ta'addanci da ba a taɓa ganin irinsa ba ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila, babu wata hujja da za ta sa a kashe fararen hula, ko ƙaddamar da hare-haren roka a kan fararen hula," in ji Mista Guterres.

Ya kuma shaida wa kwamitin cewa "yana da matuƙar muhimmanci a fahimci cewa harin na Hamas ba haka kawai ya faru ba"

Ya ƙara da cewa ''Al'ummar Falasdinawa sun fuskanci gallazawa tsawon shekara 56, ta hanyar mamayen da ya shaƙe rayuwarsu".

Ya bayyana yadda Falasdinawa suka "ga yadda shirin faɗaɗa matsugunnan Yahudawa da annobar tarzoma suka handame filayensu da kassara tattalin arzikinsu da ɗaiɗaita al'ummominsu da kuma rugurguza gidajensu".

Mista Guterres ya ƙara da cewa ya damu matuƙa kan "take dokokin ƙasashen duniya da suka shafi fararen hula da muke gani a Gaza".

Ya bayyana fargaba kan luguden wuta da Isra'ila ke ci gaba da yi wa Gaza, da kuma yawan fararen hular da lamarin ke shafa tare da "ruguza garuruwan yankin".

Ba tare da ambatar Hamas ba, Mistar Guterres ya ƙara da cewa "kare fararen hula ba zai taɓa zama amfani da su a matsayin garkuwa ba".

Haka kuma ba tare da ambatar Isra'ila ba, ya ce "kare fararen hula ba shi ne umartar fiye da mutum miliyan ɗaya su fice daga wuraren da suke zaune zuwa kudanci, in da babu muhalli, babu abinci, babu ruwan sha, babu magani, babu man fetur, sannan kuma a ci gaba da kai wa kudancin ma hari".

Babban sakataren na MDD ya yi kiran tsagaita wuta domin samun damar raba kayan agaji a Gaza cikin kwanciyar hankali, tare kuma da shiga tsakani don sakin 'yan Isra'ila da ake garkuwa da su".

Ya kuma bayyana manyan motocin agaji 62 zuwa Gaza, da ke ɗauke da abinci da magunguna tun ranar Asabar da cewa ba su kai abin da ake buƙata ba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa rashin man fetur ka iya haddasa mummunan bala'i.

Hukumar MDD da ke kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa UNRWA, ta ce matsawar babu man fetur ba za ta iya raba kayan agaji ga mutum 600,000 da ke zaune a ƙarƙashin kulawarta.

Idan babu man fetur, asibitoci ba za su samu wutar lantarki ba, ba za a samu tsaftataccen ruwan sha a famfuna ba.

Ministan harkokin waje na gwamnatin Falsɗinawa da ke Gaɓa Yamma da Kogin Jordan, Riyad al-Maliki, ya buƙaci kawo ƙarshen abin da ya kira " kisan kiyashi da sra'ila ke yi da gangan kan mutum miliyan biyu da ke zaune a Gaza.

Yayin da yake nasa jawabin ga kwamitin tsaron, ministan harkokin wajen Isra'ila ya soki Mista Guterres, yana mai tambayarsa da cewa " shin a wace duniya kake rayuwa?"

Mista Cohen ya ce kashe mutum 1,400 maza da mata da ƙananan yara da nayaƙan Hamas 1,500 suka yi a Isra'ila, sun gudanar da kisan kiyashin da "za a daɗe ba a manta da shi a tarihi ba, saboda girman muninsa", fiye da abin da ƙungiyar IS ta yi.

"Hamas ta zama sabuwar ƙungiyar 'yan Nazi," kamar yadda Mista Cohen ya ayyana. "Kamar yadda duniya ta haɗa hannu, ta ci galabar ƙungiyar 'yan Nazi, kamar yadda duniya ta haɗa kai don cin galabar ƙungiyar IS, ya kamata duniya ta mara wa Isra'ila baya don cin galabar ƙungiyar Hamas."

Yayin da yake mayar da martani kan kiran tsagaita wuta, Mista Cohen ya ce " A faɗa min shin wane martani ya kamata mayar kan kisan jarirai, da yi wa mata fyaɗe, da ƙona su da kashe ƙananan yara? Ta yaya za ka yarda da tsagaita wuta ga wanda ya sha alwashin kashe ka ko wargaza rayuwarka?

Daga baya Mista Cohen ya wallafa a shafinsa na X, da a baya aka fi sani da Twitter: "Ba zan gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ba. Saboda bayan kisan kiyashin 7 ga watan Oktoba, babu alamar tsayawa a tsakiya".

Jakadan Isra'ila a MDD ya ce Mista Guterres ya tabbatar da cewa "kwata-kwata bai san haƙiƙanin abin da ke faruwa a yankinmu ba".

"Kalamnsa na cewa ba haka kawai Hamas ta ƙaddamar da hare-harenta ba" sun bayyana fahimtar ta'addanci da kisan kai. Haƙiƙa kalamai ne da ke da wuyar fahimta. Abin takaici ne ce shugaban hukumar da ta kafu bayan kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa na 'Holocaust' ya yi irin wannan kalami", in ji Gilad Erdan.

A ranar Talata, shafin intanet na kafar yaɗa labaran Isra'ila Ynet ta ambato Mista Erdan na cewa ya sanar da jakadan ayyukan jin-ƙai na MDD, Martin Griffiths, cewa Isar'ila ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta neman biza.

"Ba zai samu damar zuwa yankin ba. Hukumominsu na buƙatar kawo sabbin mutane, musamman a lokuta irin waɗannan. Amma ba za mu amince da zuwansu ba."

Wani minista a gwamnatin Birtaniya, Robert Jenrick ya ce shugaban MDD ya yi "kuskure" kuma ya kamata ya janye kalamansa.

"Babu wanda da gangan ko akasin haka, da zai kare hare-haren ƙungiyar Hamas", kamar yadda ya shida wa kafar yaɗa labarai ta ITV.

Ya ƙara da cewa Birtaniya ba ta yadda cewa abin da Isra'ila ke yi a Gaza ya saɓa wa dokokin ƙasa-da-ƙasa.



Read full article

Source: BBC