BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Tokyo Olympics: Ahmed Hafnaoui ya bai wa duniya mamaki lokacin da ya ci kyautar zinare

Tunisia Ahmed Hafnaoui Swimmer Ahmed Hafnaoui dan Tunisia ya zama dan Afirka na farko da ya ci kyautar zinare a gasar Olympics

Mon, 26 Jul 2021 Source: BBC

Matashin nan mai wasan ninkaya, Ahmed Hafnaoui, ya ba da mamaki a lokacin da ya zama dan Afirka na farko da ya ci kyautar zinare a gasar Olympics ta 2021, bayan daga tuta a ninkayar mita 400.

Matashin mai shekaru 18, wanda shi ne karami cikin 'yan wasan da suka kai bantensu zuwa zagaye na karshe, ya ba da mamaki da irin salon ninkayarsa inda ya doke takwaransa na Australia Jack McLoughlin, wanda ya samu kyautar azurfa, sai kuma Ba'amurke Kieran Smith da ya dauki kyautar tagulla.

Hafnaoui ya shiga gasar Olympics a mataki na 15, kuma ya kai zagaye na karshe bayan fafatawa takwas, inda ya shiga jerin wadanda ba su da tabbacin nasara.

Amma tun da farko ya dage wajen ninkaya mai cike da wani salo a zagayen karshe cikin minti uku da dakika arba'in da shida, wanda saurin ya wuce irin wanda yake da shi tun da fari.

"Na yi matukar mamaki da na kai matakin karshe, na kuma yi mamaki a yanzu da nake rike da kyautar zinare a hannuna," in ji Hafnaoui.

"Na yi mamaki da na taba bangon matakin karshe, na kuma ga kaina a matsayin na farko, ban taba zaton zan kai wannan matsayin ba."

Ya kadu matuka da wannan nasara da ya yi, saboda bai ma zo da cikakkun kayan wasa ba, sannan lokacin da aka kira shi domin karbar kyautarsa, sanye yake gajeren wando da rigar shat.

A yanzu Hafnaoui shi ne dan Tunusia na biyu da ya samu kyautar gwal a wasan ninkaya a gasar Olympics, baya ga Oussamma Mellouli - wanda ya samu kyautar sau biyu, a ninkayar kilomita 10 a tseren yada kanin wani. Sai dai ba wannan ne wasa na karshe da Hafnaoui zai yi ba, zai kuma shiga ninkayar mita 800 a ranar Talata.

Kambun dai shi ne karo na biyar da Tunisia ke samun kyautar gwal a wasannin Olympic da kasar ta taba shiga.

Hafnaoui ya kara da cewa; "Kawai sai na ji hawaye na zuba daga idona - a lokacin da na ga an daga tutar kasarmu, da kuma taken kasar na tashi, wannan abin alfahari ne."

"Lokacin da na fara ninkayar, tunanin da ke raina shi ne yadda zan samu kyautar zinaren, sannan na kara sauri fiye da lokacin baya."

"Na ga dayan dan wasan Australia a ninkayar mita 200, ina jin dadi idan ina cikin ruwa, fafatawa ce mai cike da alfahari."

Sharhi: Celestine Karoney, daga sashen Wasanni a Tokyo

Ahmed Hafnaoui ya sosa zukatan mutane a ninkayar mita 400 a gasar Olympic, a lokacin da aka daga tutar kasarsa da kuma rera taken Tunisia a filin wasa na Tokyo Aquatic da ke Japan.

Dan wasan Olympic din mai shekara 18, ya jajirce har sai da ya kai bantensa, tare da zama dan Afirka na farko da ya dauki kyautar gwal a wasan Olympic na bana. Ninkayarsa ta fita daban tun lokacin da suke yi da safe, inda tsirarun mutane ne suka tafa masa a filin wasa na Aquatic saboda ba a bar 'yan kallo sun shiga ba.

Matashin ba wai ya kammala wasan ba ne kawai, yana da wata dama a ranar Talata, inda za a dawo da ninkayar mita 800.

A bayanan Hafnaoui da aka sanya lokacin cike takardunsa, an sanya shi a mataki na takwas, amma nasarar da ya samu ta sanya ya samu damar shiga gasar da ta wuce matakinsa zuwa na farko.

Dan wasan Tunisia ya fara ninkaya lokacin yana da shekara shida, a lokacin da mahaifinsa Mohammed, ya yi masa rijista a kungiyar masu wasan ninkaya, kuma yana ninkaya sau daya a kowacce rana.

Bayan shekaru 12, ya dauko wa kasarsa kyautar gwal a wasan Olympic, wadda ita ce ta biyar da kasar baki daya ta samu a tarihi.

Ya kuma sadaukar da kyautar ga iyayensa wadanda suka ba shi kwarin gwiwa da dorawa kan abin da dan kasar na farko Oussamma Mellouli ya yi lokacin da ya samu kyautar gwal a wasan na Olympics.

Mellouli, wanda zai yi wasa a zagaye na karshe, shi ne dan Tunisia na farko da ya taba samun kyautar gwal a wasan.

A yanzu dai yana da kyautar gwal guda uku da ya samu, ya kuma ce gasar Olympics ta bana da ake yi a kasar Japan, ita ce ta karshe da zai buga ya yi murabus.

"Ina da kyakkyawar alaka da Mellouli - gabanin fara wasan ya ba ni kwarin gwiwa da fatan alheri, ni ma kuma na yi masa fatan alheri a wasan da ke gabansa," in ji Hafnaoui jim kadan bayan kammala wasa.

"Gwarzo ne sosai, ina fatan wata rana na zama kamar shi."

Idan aka yi la'akari da yadda ya yi ninkaya a wannan fafatawa, alamu sun nuna Hafnaoui zai taka wani muhimmin mataki na yin nasara a wasannin da ke tafe.



Read full article

Source: BBC