BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 70 cikin 100 a Turkiyya

 124428502 Gettyimages 1239856334 Wani kasuwa a Turkiyya | Hoton alama

Thu, 5 May 2022 Source: BBC

Farashin kayan bukatun yau da kullum sun karu da kashi 70 cikin 100 a watan Afirilu, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda kididdigar hukumomi ta nuna rabon da ganin hakan tun shekara 20 baya.

Tsadar sufuri, da kayan abinci, dagado da kujeru na gyaran gida sun yi matukar karuwa, yayin da fannin sufuri ya rubanya sama da sau biyu cikin shekara guda.

Kasashen duniya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Amma matsalar Turkiyya ta shallake sauran, tun bayan shugaban kasar ya karya darajar Lira, da kin kara kudin ruwa da akan yi domin bunkasa tattalin arziki.

Farashin kayan abinci da lemukan da babu barasa a ciki sun karu da sama da kashi 89, ya yin da kayan kawata gida da suka hada da gadaje da kujeru sun karu da kashi 77.

Hukumar kididdigar Turkiyya, ta rawaito farashin kayan sun karu da kashi 7.25 a watan Afirilu.

Turkiyya ta shiga mawuyacin hali tun bayan karya darajar kudinta Lira, bayan Shugaba Tayyip Erdogan ya kafe kan kin sauya manufofin bunkasa tattalin arziki da kin fitar da kaya waje.

Matsin lambar da shugaba Erdogan ya yi wa babban bankin Turkiyya, ta janyo an samu faduwar farashi daga kashi 14 zuwa 19 a watan Satumbar bara.

A watan Afirilu an samu daidaituwar farashin kudaden waje a wata na hudu a jere, sai dai har yanzu akwai tsadar rayuwa.

Tuba Canpolat, tsohuwar jami'ar lafiya da ke zaune a Santambul, ta ce ita da iyalanta na fama da matsalolin sabod albashin mijinta baya isarsu, wanda ke aiki a kamfanin gine-gine.

Ta fara shirin komawa tsohon aikin ta, bayan daukar hutun haihuwa, amma ganin tashin farashin kudin da ake biyan masu rainon yara abin da kamar wuya.

"Ina samun abin da muke kira tagomashin da ma'aikata ke samu a Turkiyya, amma yanzu kudin bai taka kara ya karya ba, yawanci a kudin kula da jaririna daga abinci da kunzugu suke karewa," in ji ta a hira da BBC.

"Ina neman dan aiki da zan iya yi ta yanar gizo. Amma abu ne mai wuya na samu aikin da za a biya ni £5,000 na lirar Turkiyya, ya yin da farashin ke tsakanin £3,000-£4,000."

Tuba ta ce ala tilas ta koma sayan kunzugun jaririnta mai arha, sannna ba ta sauya masa a koda yaushe, farashin kayan abincin ma ya tashi.

''Ba za mu iya ba, komai ba ma iyawa sai da taimakon 'yan uwa da abokan arziki," in ji ta.

'Baudadden tsarin manufar kudi'

Charlie Robertson, mai sharhi kan sha'anin tattalin azriki a duniya, ya ce yakin da Ukraine da Rasha suka fara ya kara taka rawa wajen kara farashin kayayyaki ciki har da kayan abinci.

Har wa yau, ya ce yawancin matsalolin da Turkiyya ke fama da su, su na da nasaba da tsohon tsarin manufar bunkasar arzikin.

Sai dai wani matashin masanin tattalin ariki da ke tashe kan batun tattalin arziki, mai suna Jason Tuvey, ya ce babu alamun masu shirya manufar kudade za su bi tsarin kara kudin ruwa, ya yi hasashen hauhawar farashin kayayyakin da ake fuskanta za ta mika har kusan karshen shekarar nan.

Farashin kayayyaki na tashi cikin sauri a duniya, wannan ba ya rasa nasaba da annobar cutar korona, wadda ta janyo tashin makamashi da na masarufi.

Kasashe da dama sun maida martani da kara kudin ruwa, domin karfafawa kamfanoni da mutane daina cin bashi da tattalin abin da suke da shi da rage kashe kudade.

Bankin Ingila, ya kara kudin ruwa lamarin da aka dade ba a gani ba tun shekarar 2009, ya yin da ranar Laraba baitil malin Amurka ya sanar da karin kudin ruwa da aka dade ba a gani ba sama da shekaru 20.

Kasashe kamar Indiya, da Australia sun kure malejin bashin da suka karbo.



Read full article

Source: BBC