BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Waiwaye: An kashe 'yan Boko Haram 20, soja biyu sun rasu a hatsarin jirgi

 124264777 Mediaitem124264776 Makamai na yaki | Hoton alama

Mon, 25 Apr 2022 Source: BBC

Wannan makon ma mun duba labaran da suka fi jan hankali a Najeriya, ciki har da katin gayyatar Aisha Buhari, da ƙarin kuɗin aikin Hajji na bana, da yadda haɗakar 'yan takarar PDP na yankin Arewa ta wargaje.

Sojojin Najeriya sun rasu a hatsarin jirgin sama a Kaduna

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta tabbatar cewa matuƙa jirginta biyu ne suka rasu a hatsarin da jirgin su ya yi a Jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Jirgin ya faɗo ne a yammacin ranar Talata a wani sansanin sojan sama kuma duka mutum biyun da ke ciki ne suka rasu.

Rundunar ta bayyana sunan dakarun nata da suna Laftanal Abubakar Muhammed Alkali da Laftanal Elijah Haruna Karatu.

A yau Laraba Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru don jajanta wa dangin mutanen.

Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya ce za su yi "nutsattsen bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin".

'Kudin aikin Hajji na bana ba zai gaza Naira miliyan biyu da rabi ba'

Al'ummar Najeriya na ci gaba da tsokaci kan matakin gwamnatin Saudiyya na ware kujeru fiye da 40,000 ga maniyatta aikin Hajji na kasar.

Annobar korona dai ta hana gudanar da aikin Hajjin shekara uku da ta gabata.

A yau Alhamis ne hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta gudanar da wani taro da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi.

Alhaji Abdullahi Hardawa kwamishina ne ami kula da aikace-aikace a hukumar alhazai ta kasa, kuma ya shaida wa Ahmed Abba Abdullahi abin da aka cimma a wajen taron da aka yi a Abuja.

Aisha Buhari: Katin gayyatar 'yan takara da matar shugaban ƙasar ta aika na tayar da ƙura a Najeriya

Sunan Aisha Buhari, matar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na ta waɗari a bakunan 'yan ƙasar musamman a shafukan zumunta tun bayan da ta gayyaci 'yan takarar shugaban ƙasa na dukkan jam'iyyu zuwa buɗe baki.

Babban abin da ya fi jan hankalin 'yan ƙasar shi ne umarnin da ta bayar a katin gayyatar cewa "ba a yarda ku zo da wayoyinku ba".

'Yan takara irinsu Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu da Nyesum Wike da Farfesa Yemi Osinbajo da Chris Ngige da Bala Mohammed da David Umahi da Rochas Okorocha aka gayyata da kuma ba su umarta da kada su je da wayoyin nasu.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun yi imanin cewa matar shugaban ta koma ƙasar ce daga Daular Larabawa a farkon wannan makon gabanin tura gayyatar.

"Da gaske Aisha Buhari na gayyatar manyan mutane kar su je buɗe baki tare da wayoyinsu, wannan ai tashin hankali ne," in ji wani mai suna Dumbshroom @Dumbshroom_.

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 20, sun ceto matan da aka yi garkuwa da suShalkwatar rundunar hadin gwuiwa da ke da cibiya a birnibn

Ndjamena na kasar Chadi, wadda ta hada da sojojin Najeriya da na Nijar, ta sanar cewa dakarunta sun gudanar da samame tare da sojojin sama a yankin Tafkin Chadi.

Rundunar ta ce sojojin sama sun gano maboyar wasu mayakan Boko Haram a kusa da Tumbun Fulani da Tumbun Rago kuma sun kashe 20 cikinsu.

Sanarwar da kakakin rundunar, Kanar Muhammad Dole, ta fitar ta kuma ce bayan da sojojin sama suka gama luguden wuta, sai dakarun kasa suka kutsa wurin kuma suka fatattaki sauran mayakan na Boko Haram.

Wasu mayakan sun yi watsi da kayayyakinsu da kuma bindigoginsu kafin suka shiga cikin ruwan tafkin Chadi domin tsira da rayukansu.

Sojojin sun ga gawarwakin mayakan da samamen da aka kai ta sama ya halaka, amma wani soja ya rasa ransa a sanadiyyar hare-haren da aka kai a yankin, kuma an raunata wasu sojojin, amma an kai su wani asibitin sojoji domin ba su kulawa ta musaman.

Baya ga makaman da mayakan suka bari.

Hadakar 'yan takarar shugaban kasa hudu na PDP daga yankin arewa ta wargaje

Gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun kasa cimma matsaya kan ɗan takarar da za su mara wa baya a tsakanin wata haɗaka ta mutum hudu da suka kafa don daidaitawa wajen fitar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Gwamnan ya ce a yanzu babu batun maslaha ko kuma wani ya janye wa wani a tsakanin masu neman takarar.

Gwamnan ya ce kafin wannan lokaci an yi tunanin tsakaninsa da Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da Muhammad Hayatudeen da duk ke neman tikitin takara a inuwar PDP na iya maslaha a tsakaninsu.

Sai dai lura da yadda abubuwa ke tafiya kowa kawai tashi ta fisshe shi.

Gwamnan na wannan kalamai ne bayan wata sanarwar da ya fitar a yammacin jiya Juma'a tare da jaddada cewa a shirye yake a fafata da shi a zaben 2023.

"Mun zauna mu hudu 'yan takara wadanda a kashin kanmu muka yi matsayar cewa za mu tattauna mu yi sulhu a tsakaninmu, muka duba muka tattauna muka yi matsayar cewa abunda mu ke yi ga dukan alamu ya ci- tura.

Siyasar Kano: Yadda Kwamishinonin Ganduje ke murabus domin neman takara a zaben 2023

Masu muƙaman siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da ajiye mukamansu saboda sha'awar fitowa takara a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar ga masu sha'awar tsayawa takarar a kan su sauka daga duk wani mukami na gwamnati.

Wani ɗan jarida da ke gabatar da shirye-shiryen siyasa a jihar ta Kano, Bashir Sarki, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu kusan mutum tara sun ajiye mukamansu tun bayan umarnin gwamnan.

Ya ce cikin waɗanda suka ajiye aiki zuwa yanzu, har da Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan Kano wanda ya sauka daga matsayin Kwamishinan Noma; da Murtala Sule Garo, Kwamishinan Kananan Hukumomi, da na Raya Karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso.

Akwai kuma Nura Muhammad Dankade, Kwamishinan Kasafi da Kwamishinan Ilimi, Sunusi Sa'idu Kiru.



Read full article

Source: BBC