BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Wasu manyan ƴan siyasa da ke son gadar kujerar Shugaba Buhari

Buhari Buhari Nig Shugaba Muhammadu Buahri

Sat, 16 Apr 2022 Source: BBC

Yayin da babban zaben da zai samar da shugaban kasa a Najeriya ke kara matsowa, BBC ta yi nazarin wasu 'ya siyasa da suka bayyana sha'awarsu ta tsayawa takarar mukamin shugaban kasar.

A wannan karon, mun duba wasu 'yan siyasar da yawancinsu sun fito ne daga wasu jam'iyyun siyasa da ba sa cikin manyan jam'iyu na APC mai mulkin Najeriya da ta PDP wadda ita ce babbar jam'iyar adawa a kasar.

Ga 'yan siyasa takwas masu sha'awar maye gurbin shugaba mai ci, Muhammadu Buhari bayan wa'adin mulkinsa ya kare a shekarar 2023.

Rabi'u Musa Kwankwaso

An haifi Muhammad Rabi'u Musa Kwankwaso a ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba na 1956, a kauyen Kwankwaso da ke a kasar karamar hukumar Madobi ta jihar Kano ta Najeriya,

Rabiu Musa ya halarci makarantar kere-kere da ke a garin Wudil da kuma kwalejin fasaha ta Kano bayan nan ya karasa makarantar Kaduna Polytechnic da ke a garin jihar Kaduna.

Fitaccen dan siyasa a Najeriya ne, ya rike matsayin gwamna a jiar Kano har sau biyu, wato a shekara ta (1999 zuwa 2003), da kuma shekara ta (2011 zuwa 2015).

Shi ne kuma gwamnan farko na jihar Kano a jamhuriya ta hudu kuma ya ci zabe ne duk a karkashin jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya sauya sheka ya koma jam'iyyar APC.

A zaben shekara ta (2003), Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rashin nasara ne a hannun Malam Ibrahim Shekarau.

A watan Yuli a shekara ta 2003, Olusegun Obasanjo ya nada shi a matsayin ministan tsaron Najeriya bayan rashin nasara da ya yi a zaben.

A shekara ta 2015, Kwankwaso ya yi rashin nasara a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, daga bisani sai ya sake sauya sheka zuwa takarar kujerar Sanata wanda a nan ne ya samu nasarar cin zaben.

A shekara ta 2018, ya fice daga jam'iyyar ta APC inda ya sake komawa jam'iyyar PDP da niyyar yin takarar Shugaban ƙasa, sai dai ya sha kaye a hannun abokin karawarsa Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani wanda aka gudanar a garin Fatakwal.

Kwankwaso ya rike mukamai da yawa a Jahar Kano dama kasar Najeriya baki daya, wadanda suka hada da aikin gwamnati da na siyasa baki daya.

  • Mataimakin Kakakin Majalisar Dattawa a watan Janairu a shekara ta 1992) zuwa watan Nuwamba a shekara ta 1993.


  • Gwamnan Jihar Kano 29 ga watan Mayu a shekara ta 1999) zuwa 29 ga watan Mayun shekara ta 2003


  • Ministan Tsaro na Kasa watan - Yuli shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2007


  • Babban Jakadan Najeriya a Dafur A shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2011
  • Gwamnan Jahar Kano - 29 ga watan Mayu a shekara ta 2011 zuwa 29 ga watan Mayu a shekara ta 2015


  • Sanatan Kano ta Tsakiya - 11 ga watan Yuni a shekara ta 2015 zuwa shekara ta 2019


  • Tsohon gwamnan Jihar Kanon ya sake ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa ta NNPP.

    Sai dai dama Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa a lokacin da yana PDP amma ya soma tattauna wa da jam'iyyar NNPP domin sauya sheka, amma a ranar Talata 29 ga watan Maris tsohon gwamnan kuma tsohon ministan tsaro a kasar ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya ta NNPP.

    Bayan wannan lokacin ne ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin sabuar jam'iyyar da ya koma, wato NNPP.

    Tunde Bakare

    Tunde Bakare ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a shekarar 2011.

    Sai dai bayan wannn lokacin, Fasto Tunde Bakare, ya ce gwamnatin shugaban kasar ta jefa Najeriya a halin ci baya maimakon ci gaba.

    Tunde Bakare fasto ne a cocin The Citadel Global Community Church (CGCC) a Najeriya. Ya ce tun da farko an haife shi Muslmi ne amma daga baya ya shiga addinin Kirista a 1974.

    Bakare ya halarci jami'ar Legas tsakanin 1977 zuwa 1980, kuma ya zama lauya bayan da ya halarci makarantar lauyoyi a 1981, inda ya fara aiki da shahararren lauyan nan Gani Fawehinmi da Rotimi Williams & Co da kuma Burke & Co, Solicitors.

    Daga baya ya bude na shi ofishin mai suna Tunde Bakare & Co (El-Shaddai Chambers) a watan Oktoban 1984.

    A watan Mayun 1988 ya sauya sheka inda ya bar aikin lauya kuma ya kafa cocin nasa.

    Tun bayan raba gari da suka yi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Tunde Bakare ya ci gaba da hada siyasa da aikinsa na fasto, kuma yana cikin 'yan Najeriya da ake sa ran za su taka rawa a zaben shugaban kasa na 2023.

    Sai dai zuwa yanzu bai bayyana sunan jam'iyyar siyasar da zai tsaya takara a karkashinta ba.

    Kingsley Moghalu

    Kingsley Chiedu Moghalu sanannen dan siyasa ne wanda ya taba tsayawa takaraa mukamin shugaban kasa a zaben 2019.

    An haife shi ne a jihar Legas a 1963 kuma ya girma ne a kasasshen Switzerland da Amurka inda mahaifinsa ya yi aiki.

    Masani tatalin arziki ne, inda ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya a karkashin gwamnatin Umaru Musa Yar'Adua daga 2009 zuwa 2014.

    Y akafa wani kamfani mai zaman kansa mai suna Sogato Strategies LLC a birnin Geneva, kamfanin da ke bayar da shawara kan yadda ake zuba jari a kamfanoni. bayan da ya bar aikin da yayi a Majalisar Dinkin Duniya.

    Daga baya ya koyar a jami'ar Tufts daga 2015 zuwa 2017.

    A halin yanzu shi ne dan takarar mukamin shugaban kasa a jam'iyyar Young Progressives Party (YPP), takarar da ya dade yana yi tun zaben 2019.

    Omoyele Sowore

    An haifi Omoyele "Yele" Sowore ne a shekarar 1971, kuma mutum ne da ya shahara kan faftukar kare hakkin dan Adam baya ga aikinsa na jarida da kuma zama dan siyasa karkashin jam'iyyar da ya kafa mai suna African Action Congress.

    A watan Agustan 2019, hukumomin Najeriya sun kama Sowore kan tuhumar cin amanar kasa bayan da ya jagoranci wata zanga-zaga mai suna RevolutionNow. An sake kama shi daga baya a birnin Abuja bayan da ya sake shirya wata zanga-zangar a wata Janairun 2021.

    Ya halarci jami'ar Legas daga 1989 zuwa 1995, inda ya karanci fannin Geography, kuma an taba kara ma karatun nasa tsawon shekara biyu saboda fafutukar kare hakokin 'yan makaranta da rika yi.

    Ya rike mukamin shugaban gwamnatin dalibai ta jami'ar Legas daga 1992 zuwa 1994, kma yana da digiri na biyu a fannin mulki, wanda ya samo daga jami'ar Columbia University ta kasar Amurka.

    Sanannen dan gwagwarmaya ne a Najeriya kuma hukumomin tsaron kasar sun sha damke shi kan ayyukansa na nema wa jama'a 'yancinsu.

    A shekarar 2006, Sowore ya bude jaridarsa mai suna Sahara Reporters a birnin New York domin ci gaba da yaki da abin da ya ke kallo matsalar ci hanci da rashin iya mulki ne. Gwamnatin Amurka ce ta ba shi wani tallafi karkashin gidauniyar Ford Fundation da kuma Omidyar Foundation.

    A wata Fabrairun 2018, Sowore ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019, inda ya kafa jam'iyyar African Action Congress (AAC), kuma har zuwa wannan lokaci shi ne dan takarar jam'iyyar wanda ake sa ran zai tsaya takara a zaben 2023.

    Khadijah Okunnu-Lamidi

    Khadijah Okunnu-Lamidi ita ce mace ta farko da ta fito fili ta bayyana sha'awar tsayawa takarar mukamin shugaban kasa a zaben 2023.

    Shekarun Khadijah 38 da haihuwa, kuma an haife ta ne a jihar Legas, kuma mahaifinta shi ne Lateef Olufemi Okunnu, tsohuwar ministan ayyuka a tsohuwar gwamnati farar hula.

    Babban abin da aka fi saninta a kai shi ne na kafofin yada labarai.

    A bangaren ilimi, Khadijah ta halarci jami'ar Boston da jami'ar Heriot-Watt University wadanda dukkansu ke da rassa a Dubai inda ta sami digiri na daya da na biyu.

    Khadijah Okunnu-Lamidi ta kafa wani kamfani mai suna Slice Media Services mai harkar yada labarai da tallace-tallace a Najeriya.

    Adeshola Lamidi, wani kwararre ne kan harkar kasuwanci zamani da zuba jari ne mai gidanta kuma suna da 'ya'ya tsakaninsu.

    A ciin watan Afrilun 2022 ta shiga jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), wadda ta ce ra'ayinta ya yi daidai da manufofin jam'iyyar.

    Nicolas Felix

    Dr. Nicolas Felix dan siyasa ne mai shekara 41 da haihuwa, kuma an haife shi ne a birnin Auchi na jihar Edo a kudanci Najeriya.

    Shi ne shgaban kamfanin Miracle Center International, da Zoe Homecare Agency da Victory Security Company da wasu kamfanonin.

    Ya halarci makarantar tarayya ta Federal Polytechnic, Auchi jihar Edo, kuma yana da digiri na biyu da na uku daga jami'ar Ames Christian University a birnin Florida na Amurka, da kuma jami'ar CICA International University & Seminary a jihar New York ta Amurka.

    Dr. Nicolas Felix shi ne dan takarar jam'iyyar siyasa ta Peoples Coalition Party of Nigeria PCP kuma yana cikin matasa masu karancin shekaru da ke fafutukar ganin tafarkin dimukradiyya ya wanzu a Najeriya.

    Mazaunin birnin New York ne na Amurka, kuma ya ce yana da yakinin warware matsalar karancin hasken lantarki da ta addabi Najeriya.

    Mojisola Adekunle-Obasanjo

    A haifi Mojisola Adekunle-Obasanjo a ranar 10 ga watan Agustan 1944, kuma mace ce da ta yi aikin soja har ta kai ga mukamin manjo a rundunar sojin Najeriya.

    Ita ce ta kafa jam'iyyar Masses Movement of Nigeria a 1998 kuma ta tsaya takarar mukamin shugaban kasa karkashin inuar wannan jam'iyyar wadda ake kira da takaitaccen sunan MMM a 2003.

    Ita ce kuma mace daya tilo da ta tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2007 a Najeriya.

    Mojisola Adekunle-Obasanjo tsouwar matar shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ce.

    Ta taba yin aiki a matsayin ma'aikaciyar lafiya a rundunar sjin Najeriya kafin daga baya ta amince ta tsaya takara a 2003.

    A bana ma ta bayyana aniyarta ta yin takara karkashin jam'iyyarta ta Masses Movement of Nigeria.

    Chukwuka Monye

    Chukwuka Monye shi ne mutumin da ya kafa kamfanin Ciuci Consulting a Najeriya, kuma ya dade yana yin ayyuka kan samar da hanyoyin inganta rayuwar jama'a.

    A haife shi a watan Yulin 1979, kuma yana alfahari cewa shi dan Najeriya ne, wada duk da cewa ya sami damar komawa wata kasar da sauya kasarsa ta asal, har zuwa wannan lkacin fasfon Najeriya ne kawai yake rike da shi.

    Ya halarci makarantar sakandarensa ne tare da dalibai daga wasu jihohin Najeriya inda ya kulla alaka da yawancinsu.

    Ya fara halartar jami'ar jihar Ogun kafin daga baya ya koma Amurka inda ya halarci jami'ar Warner University. Yana kuma da digiri na biyu daga jam'ar Oxford University.

    Yana fatan zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar African Democratic Congress.

    Chukwuka Monye ya ce cikin aubuwan da yafi so akwai yin wake-wake da raye-raye da kidan gangunan konga.

    Yana kuma sha'awar buga kwallon kwando da na golf.

    Mazaunin birnin Asaba na jihar Delta ne, inda yake zama tare da mai dakinsa da 'ya'yansu biyu.



    Read full article

    Source: BBC