BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Yadda rayuwar wani direba ta sauya bayan mayar da dala 50,000 da ya tsinta

 123939982 Pupilliberia Emmanuel Tuloe, direba da ya ci anfanin rike gaskiya

Mon, 4 Apr 2022 Source: BBC

Labarin abin da ya faru da dan kasar Laberiya Emmanuel Tuloe ya yi kama da tatsuniya a wannan zamani.

Matashin mai shekara 19 da ke sanye da kayan makaranta masu launin shudi, ya fi kowa girma a ajinsu, akalla ya girmi mafi yawan yaran da shekara shida.

Matsahin da ya daina makaranta tun a matakin firamare yanzu yana cike da farin ciki.

A bara, yana ta fadi-tashin yadda zai samu kudaden da zai dinga rayuwa da su, ya tsinci dalar Amurka 50,000 tare da wasu kudaden Laberiya a kunshe cikin wata leda lokacin yana aikin tasi a gefen titi.

Da ya ga dama da sai ya boye kudin duk da dai ba su kai sun kawo ba. Amma sai ya gwammace ya bai wa wata yar uwarsa ta ajiye, lokacin da mai kudin ya bayar da cigiya a gidan radiyon kasar, sai Emmanuel ya kai masa.

Abokansa sun dinga zolarsa kan wannan amana da ya nuna - suna cewa zai mutu cikin talauci in bai yi wasa ba - amma wannan abu da ya yi ya janyo masa yabo da ci gaba, ciki har da samun gurbin karatu a makarantar Ricks Institute, daya daga cikin makarantu mafiya daraja a Laberiya.

Shugaban kasar George Weah ya bai wa matashin dala 10,000. Haka shi ma mai gidan rediyon ya ba shi kudade da masu kallo suka tara. Mai kudin ya ba shi dala 1,500 kyauta.

Mafi mahimmanci cikin wadannan shi ne wata Jami'a a Amurka ta yi masa alkawarin gurbin karatu kyauta da zarar ya kammala sakandire dinsa.

'Jin dadin tsarin ilimi'

Abin da ya mayar da hankali kenan ya yi a Ricks, makarantar kwanan da aka kafa kusan shekara 135 baya wadda ta yaran masu hali ce da suka samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka tun da farko. Gininta hawa biyu ne, kuma kujerunta masu taushi ne. Tazararta da kogin Atlanta kilomita shida ne kacal.

"Ina jin dadin makaranta, ba wai don Ricks ta yi suna ba, a'a, saboda horo da tarbiyya da ake bayarwa a fannin koyo, " In ji Emmanuel.

Kamar dai yadda yanayi ke tilasta wa mafi yawan yara masu rangwamen gata a Laberiya, shi ma ya bar makaranta yana da shekara tara, ya fara neman kudi domin taimaka wa 'yan uwa da iyayensa.

Jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa a wani hadarin jirgin kwale-kwale, hakan ya sa ya koma zama da wata 'yar uwarsa.

Shekaru kadan sai ya fara tuka tasi.

Saboda jimawa da ya yi baya makaranta shi yasa yake bukatar kulawa ta musamman.

Ko da ya fara zuwa makaranta aji shida, ya dinga jin cewa shi kaskantacce ne; ba ya iya magana ko kadan amma a hankali muka rika taimaka masa", kamar yadda malamin Tamba Bangbeor ya shaida wa BBC.

"A tsarin makaranta, bai samu fandisho mai kyau ba, don haka muka sanya shi cikin wani shiri na musamman da zai rika taimaka masa."

Yanzu yana da shekara shida da zai yi a sakandire, ma'ana zai kammala yana da shekara 25. Amma banbancin shekaru bai damunsa tsakaninsa da 'yan ajinsu da yake kira "abokansa".

Ya ce rayuwar da yake a makarantar kwana da dadi wata haya ce ta koyon yadda mutum zai iya rayuwa a gaba shi kadai.

'Yana da kyau ka zama mai gaskiya'

Da yake magana kan yadda mutane suka rika tsokanar shi bayan mayar da kudin sai ya ce, da zan iya boye su na yi abin da nake so, amma da ban samu wannan damar da nake da ita ba a yanzu.

Emmanuel ya yi wa Allah godiya da ya ba shi wannan dama haka kuma ya "godewa iyayensa da suka koya masa gaskiya".

"Sakona ga matasa shi ne: yana da kyau ka zama mai gaskiya; kada ka dauki abin da ba naka ba."

Su kansu malaman makaranta Ricks na farin cikin samun Emmanuel a matsayin dalibinsu.

"Muna amfana da shi ba kawai dan ya kasance mai gaskiya ba, kuma shi ne mai tsaron raga na biyu a tawagar makarantar," in ji Mr Bangbeor

Yan ajinsu sun rika murna da kasancewarsa a ajin.

Bethlene Kelley, mai shekara 11, ya ambace shi da "babban aboki da mai cika magana ba amma yana da nuna damuwa kan mu, muna girmama shi da ganin kimar shi."

Caleb Cooper mai shekara 12 ya ce Emmanuel na da kirki ya ji dadin haduwa da shi a matsayin wanda suke kwana wuri guda.

"Ba ya satar kayan mutane," in ji Caleb.

Da yawan abokansa da ya yi aikin tasi da su ba su yi masa bakin ciki da rayuwar da yake ciki a yanzu ba.

Daya daga cikinsu mai suna Lawrence Fleming dan shekara 30, ya shaida wa BBC cewa ya bar makaranta ne a irin shekarun da Emmanuel ya bari.

"Abin jin dadi ne cewa Emmanuel ya koma makaranta, muna ji masa dadi,"in ji shi.



Read full article

Source: BBC