BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

'Yan Real Madrid da suka je Braga buga Champions League

Real Madrid Goal Celebration Yan wasan Real Madrid

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Real Madrid ta ziyarci Braga, domin buga wasa na uku a cikin rukuni a Champions League ranar Talata.

Wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin biyu za su fafata a gasar ta zakarun Turai a tarihi.

Wasan da za a buga a Municipal Stadium, Real Madrid ce ta ɗaya a rukuni na uku da maki shida, sai Napoli mai maki uku da Braga itama maki uku da kuma Union Berlin mara maki ko daya.

A dai ranar Talata FC Union Berling za ta karɓi baƙuncin Napoli a ɗaya wasan rukuni na ukun

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Diego Pineiro.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rudiger da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde da kuma Tchouameni.

Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.



Read full article

Source: BBC