BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

'Yan bindiga sun kashe 'sama da mutum 40' a Zamfara

 118771378 Zamfaragovernordissolvescabinet Bellomatawalledonsackallimcommissionersforstateexecutivec Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle

Sat, 10 Jul 2021 Source: BBC

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a jerin hare-hare da suka kai a wasu kauyukan jihar.

Lamairn ya faru ne a kauyuka fiye da biyar da ke karamar hukumar Maru da ranar Alhamis sai dai bayanai ba su fito ba sai Juma'a.

Ganau sun shaida wa BBC cewa maharan sun je kauyukan Gidan Adamu, Gidan Maidaji, Bauci, Wari, Kyara da Gidan Maidawa kan babura sannna suka bude wuta.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum arba'in da biyu, a cewar wani mutum da muka tattauna da shi.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da kai harin, sai dai ta shaida wa BBC Hausa cewa mutum 35 aka kashe.



Read full article

Source: BBC