BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Yan sandan Najeriya sun kama mutum 30 da ƙwace bindiga 23

Gunmen Attack Security Operatives In Nigeria.png Yan sanda sun addabe ya Najeriya musamma a arewacin kasa

Fri, 18 Mar 2022 Source: BBC

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu nasarar kama mutum 30 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da garkuwa da mutane da fashi da makami da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba da satar mota da fyaɗe da sayen kayan sata.

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya jinjina wa runduna ta musamman ta Force Intelligence Bureau Special Tactical Squad da aikin kama waɗannan mutane.

Ƴan sandan sun samu nasarar ƙwato bindigogi takwas waɗanda aka ƙera a ƙasar waje sai kuma AK47 ƙirar gida, da kuma kananan bindigogi takwas da harsasai 2,200.

Haka kuma ƴan sandan sun ƙwato jigida ta AK47 guda 12 da motoci uku na sata da lambobin mota 10 na bogi da kuma kuɗi naira miliyan daya da dubu ɗari takwas da tamanin daga waɗanda ake zargin.

Cikin manyan waɗanda ake zargin da aka kama akwai wani Ahmed Yunusa wanda aka fi sani da "Yellow Ashana" mai shekara 36 wanda ake zargi yana daga cikin wani gungun ɓarayi da ke addabar ƙauyuka da matafiya kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Jami'an sun daɗe suna nemansa inda ya gudu tun bayan wani samame da ƴan sandan suka kai da ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin ƴan fashi mai suna Yellow Magaji wanda aka fi sani da Arushe.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce gungunsa ya yi garkuwa da mutane da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma ƙaddamar da hare-hare a kan al'ummar Kadara da ke Jihar Kaduna inda aka kashe mutane da dama.

Ya kuma amsa cewa su suka yi garkuwa tare da kashe wata Hafsat Isah wadda wata ƙawarta ce ta ja ta inda ta kai ta sansanin masu garkuwan, amma daga baya an kama ta.

Cikin waɗanda aka kaman akwai wata Mrs Nvou Michael mai shekara 37 daga Ƙaramar Hukumar Vom ta jihar Filato wadda jami'an suka kama a kan hanyar Saminaka zuwa Jos inda aka kama ta da bindigogi 15 ƙirar gida da harsasai 400 a cikin wata mota ƙirar Bas.

Bincike ya nuna cewa wadda ake zargin dillaliyar makamai ce wadda ke kai wa ɓarayin daji makamai a Jihar Kaduna.

Haka kuma jami'an tsaron sun kama wani Nuhu Yakubu mai shekara 33 daga Donga a Jihar Taraba a lokacin da yake safarar harsasan AK47 1,500 daga Wukari zuwa dajin Donga.

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya sha alwashin kawo ƙarshen irin waɗannan ayyukan da kuma ganin bayan masu irin waɗannan halaye wanda ya ce suna kasancewa barazana ga tsaron Najeriya.

Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar da su taimaka wa jami'an tsaro da bayanan sirri da za su kai ga kama masu aikata irin waɗannan laifuka.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: