BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Yau ce ranar masu lalurar Zabiya ta duniya

 118908626 6513ce50 E7d7 4130 Bc4c D62b2366f80e Kowacce ranar 13 ga watan Yuni ne ranar tunawa da masu lalurar zabiya a duniya

Sun, 13 Jun 2021 Source: BBC

Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 13 ga watan Yuni a matsayin ranar tunawa da miliyoyin masu lalurar zabiya a duniya. Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna a duk mutum 17,000 ana samun zabiya guda.

Ana dai tunawa da masu larurar ne musamman saboda irin halin kunci, da kyama da al'umma ke nuna musu yawanci tun daga lokacin kuruciya har zuwa girma.

Baya ga wannan hali da sukan samu kansu a ciki a tsakanin al'umma, masu lalurar zabiya na kuma fama da larurar fata da ta idanu. Da zarar sun shiga rana fatarsu kan yamushe ta kuma sauya launi zuwa Jajur tamkar wani abu ya kona musu fata.

Harwayau zabiya na fama da lalurar rashin karfin gani, tun daga kankantar shekaru har zuwa girmansu, ta yadda su na fuskanar matsalar karatu a makaranta sakamakon yadda indai ba a yi rubutu gwara-gwara yadda za su iya gani ba.

Albarkacin wannan rana abokin aikinmu Usman Minjibir ya tattauna da wasu masu lalurar zabiya guda biyu a Najeriya, da suka bayyana irin halin da suke samun kansu a ciki sakamakon lalurar da suke fama da ita.

Daya daga cikinsu mai suna Donald Tempe, ya bayyana cewa shi da abokin tagwaitarsa sun kasance Zabiya, kuma iyayensu bakken fata ne ba su da lalurar zabiya.

''Lokacin da muna yara mun sha wuya acikin wuya, saboda yadda idan mu na wasa da yara 'yan uwanmu, sai su ki yadda su yi wasa da mu su na cewa ba sa son wasa da mu domin kar mu shafa musu lalurar.

A lokacin da muke makaranta ma mun sha wuya saboda mu na da matsalar gani, allon ajin na mu na can da nisa ba ma ganin rubutu saboda kankanta, don haka dole sai mun koma gaba ko mu zauna kasa. lokacin malaman ba su gane matsalarmu ba, har shugaban makarantarmu kan kora mu, domin mu koma can baya mu zauna,'' Inji Donald.

Sai dai akwai banbancin kuruciya tsakanin Donald da Laurence Mary, domin ita ta samu gata sosai daga iyayenta yadda ko yaya ba sa barin wani ya taba su ita da 'yar uwarta da suke da lalura iri guda.

Sai dai sun yi tarayya a matsalolin da suka fuskanta a makaranta musamman a lokacin da ta shiga makarantar gaba da sakandare, ta ce ta sha wuya ba kadan ba,''saboda lokacin mahaifinmu baya nan, daman a lokacin mu na firamare shi ya ke bibiya domin tabbatar da cewa ba mu sha wuyar karatu ba.

Lokacin da na shiga sakandare ba na iya zuwa kujerar gaba na zauna saboda ina jin kunya, sai akai ta fadawa mahaifiyata cewa ba na iya rubutu da kyau, na wahala matuka sai dai na karbi littafin abokan karatuna na kwafa, wannan ya shafi kwazona sosai.''

Laurence ta ce ana yawan cewa gishiri na bata musu fata, ta ce ba haka ba ne abin da ke bata musu fata ita ce rana. ''Ina bai wa masu lalurar mu shawarar su dinga rufe jikinsu da hijabi ko doguwar riga yadda rana ba za ta yi wa fatar mu illa ba, saboda idan fatar na fama da lalura irin haka to cutar Kansa za ta kama mu kuma maganin ta sai masu hannu da shuni.''

A karshe sun yi kira ga gawamnati ta kawo musu dauki musamman matsalar rashin karfin gani, saboda gilashin kara karfin gani da ake yi musu ya na da matukar tsada.



Read full article

Source: BBC