BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Zaɓen 2023: PDP ta ce ba za ta ba wa wani yanki takara ba

 124700632 Mediaitem124700631 Mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PDP Ibrahim Abdullahi

Thu, 12 May 2022 Source: BBC

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP, ta ce babu wani yanki da za ta kebe wa takarar shugabancin kasar a zaben 2023.

Shugabannin jam'iyyar sun cimma wannan matsaya ne a karshen taron da suka kammala a tsakar daren da ya gabata, na Laraba, a Abuja, inda jiga-jigan jam'iyyar da dama suka halarta suka kuma amince da wasu babutuwa da dama.

Sai dai a hirarsa da BBC mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PDP Ibrahim Abdullahi, ya ce a yayin taron 'yan yankin kudu maso gabashin kasar, wato 'yan kabilar Igbo, sun yi roko da a ba su damar fitar da dan takara daga yankin, amma, taron bai amince da haka ba, inda aka zartar da cewa kowanne daga cikin sassan kasar shida yana da damar fitar da mai neman takara.

Jami'in ya ce, ''Tsohon ciyaman na jam'iyyar ta mu Okwesilieze Nwodo, ya dan nemi cewa, duk da dai sun ba jam'iyyar nan goyon baya, kuma suna kawo kuri'u kusan fiye da duk wani bangare na Najeriya wadannan shida da ake da, kuma suna rokon a dan taimake su a ba su takara.

''Amma wannan magana ce ta girma da arziki wadda ya nema ne ya roka, inda hali a yi musu, amma sun kai ga amincewa da matsaya ta jam'iyya na cewa za a bar takara ga kowa dan Najeriya, duka bangarorin shida na Najeriya kowa ke da hajarsa na neman shugabancin kasar ya fito ya yi tallar kansa.'' In ji shi.

Sai dai ya ce yana iya yuwuwa a can gaba kafin a yi zabe jam'iyya ta ga ya kamata sauran mutane su janye wa mutum daya, amma kuma wannan za ta kasance ne yarjejeniya tsakanin 'yan takara, amma dai a yanzu kowane dan Najeriya ya ce yana da hakkin ya nema.

Ya ce, batun maganar karba-karba ko ware kujerar shugabancin Najeriyar ga wani bangare na kasar ba ya cikin tsarin mulkin jam'iyyarsu, abu ne kawai na girma da arziki, na yarjejeniya.

Dangane da yadda wasu ke kallon kamar jam'iyyar tana dabara ne, ta hanyar jinkiri ta ga wanda abokiyar hamayyarta, jam'iyya mai mulki APC za ta fitar da dan takararta, mataimakin sakataren na PDP ya ce sam-sam ba haka abin yake ba.

Ya ce watakila su dai APC ne suke wannan amma su ba wani abu da za su jira su gani daga abokiyar hamayyar tasu.

''To taku wane iri kake jira ka gani daga mutanen da suka sa kasa a cikin wannan hali na ha'ula'i.'' In ji shi.

Ya kara da cewa su yanzu a APC abin da suke yi shi ne sai sun tsaya sun tantance, domin gudun kwatanta kura-kuran da suka yi a baya, domin su yi abin da zai zama maslaha ga 'yan Najeriya, sakamakon mawuyacin halin da ya ce APC ta jefa kasar.

Masu neman takara

Zuwa yanzu sama da mutane goma ne suka bayyana aniyarsu ta neman yi wa jam'iyyar ta PDP takarar shugabancin Najeriyar a zaben da za a yi a 2023.

Kuma hudu daga cikin gwamnoni 19 na jam'iyyar na daga cikin masu nema, hadi da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.



Read full article

Source: BBC