BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Zamantakewa: Matakan da amarya za ta bi don kyautata mu'amalarta da uwargidanta

 119330779 Zamantakewa Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa kan yanayzin zamantakewar mutane

Sat, 10 Jul 2021 Source: BBC

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayzin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na ukun, shirin ya yi duba ne kan yadda amare za su gyara zamantakewarsu da uwayen gidajensu da sauran mutanen gida.

Ina amarya? Wannan makon naki ne kamar yadda na yi alƙawari.

Amarya mai maganar suga komai ta fada a suga yake in ji Hausawa, amma fa kar ki ruɗu ki dinga fadar abin da ba shi ne ba.

Na san a satin da ya gabata kin taya uwargida jin dadin shawarwarin da aka ba ta na yadda za ta kyautatawa zamantakewarta da ke.

To ke ma yau ya kamata ki daure ki karbi shawarwarin da za a ba ki ko da masu ɗaci ne, kin san dama ita gaskiya ɗaci gare ta.

A duk lokacin da namiji ya zo neman aurenki kuma ya kasance mai iyali ne, to mataki na farko shi ne kar ki ruɗu da maganganunsa na kushe matarsa ko sauran matansa.

Duk namijin da kika ga ya je neman karin aure ba wai don ba ya son ta gida ba ne, 'a'a su maza haka aka halicci zuciyarsu za su iya adana son mace fiye da daya a cikinta, kuma shari'a ta ba su damar ƙari.

Kar ki dagawa kanki hankali da neman sanin halin da matarsa ke ciki, hakan ka iya dagula maki lissafi, don watakila za ki iya jin abin da ba lallai ya yi maki dadi ba.

Ke dai ki je da tsarkakakkiyar zuciya, ki zauna lafiya da shi da matarsa da ƴaƴansa da danginsa da abokan arzikinsa, ki kuma so su don Allah.

Surayya Inuwa Yahaya Kofar Mata wata ƴar jarida, mai gabatar da jawabai a wuraren taruka wato MC sannan kuma matar aure da ta je a matsayin ta biyu, ta bayyana wasu matakai da ya kamata duk mai shirin auren mai mata ta yi la'akari da su don kyautata zamantakewarta.

Lokaci zai zo da miji zai ta ba ki labari kala-kala yana ce mkiki ke ce gimbiy, ke ce sarauniya da sauransu, a lokacin da yake faɗa, ki ji don jin dadi kawai amma kar ki saka shi a ranki don kin fi waccar ne, don ita ma zai iya gaya mata hakan.

Surayya ta ce ba za ta manta shekarun baya da aka zo aurenta ba, inda mahaifiyarta da kanta ta ce mata ta kwantar da hankalinta ta ci arziƙin uwargidanta da za ta je ta samu.

"Kuma da na yi hakan na ga hasken abin, ba wata asara da na yi ta yin hakan sai ma kwanciyar hankalin da na samar wa raina," a cewarta.

Shi ma Malam Ibrahim Khalil malamin addinin Musulunci a Kano ya ce amare su sassauta zuciyoyinsu su tausaya wa uwayen gida a lokacin da za su je su same su.

"Ki sa a ranki idan ke ce uwargida ke ma za ki kasance cikin ƙunci don haka ki tausaya wa wata ke ma," in ji Malam.

Ya kuma ba da shawarar cewa da zarar miji ya ɗauko maganar matarsa don kushe ta , to ki yi maza ki tare shi da cewa 'gaskiya bai kamata ka dinga muzanta uwargidanka ba, kamta ya yi ka girmamata,' kamar yadda Malam ya ƙara da cewa.

Ga wasu matakan a sauƙaƙe da za ki don inganta zamantakewarki a matsayinki na wadda kika tarar da wata a gidan:

  • Ki zama mai yawan sauraro ba mai yawaita magana ba


  • Ki zama mai adalci da karamci


  • Ki dinga yawan yi wa miji da abokiyar zama da 'ya'yansu uzuri


  • Ki zama mai dauke kai kan kananan abubuwa


  • Ki bai wa uwargida girmanta ban da raini


  • Kar ki zama mai yawan kai ƙara da ƙorafi, ki dinga warware matsalolinki a siyasance cikin diflomasiyya, sai dai ki guji siyasar munafunci
  • Amma a inda kika ga za a zalince ki da yawa to ki magantu don a yi sulhu a wuce wajen.




  • Read full article
    Source: BBC