BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Yadda ɗan shekara 18 ya kashe matar aure da taɓarya a Kano

 123862809 277300984 4572837339484986 3906780456294747615 N Abdulsamad Suleiman ne wanda ake zargi da aikata kisan

Wed, 30 Mar 2022 Source: BBC

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 18 bisa zarginsa da kashe matar aure a Jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun yan sanda reshen Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Kumbotso.

Wanda ake zargi da aikata kisan mai suna Abdulsamad Suleiman, ya amsa laifin ga ƴan sandan inda ya ce tun da farko ya shiga gidan matar inda ya same ta a kan gado, bayan ya gaishe ta sai ya ga wayoyi uku sa'annan ya sace su, in ji kakakin 'yan sndan.

SP Kiyawa ya kara da cewa, bayan matashin ya gano cewa matar ta gane shi, sai ya yi amfani da taɓarya ya yi ta buga mata a kai, haka kuma ya buga wa ƴaƴanta biyu taɓaryar sa'annan ya gudu da wayoyin.

Bayan gudanar da wannan aika-aika ne mijin matar ya je ya samu matarsa ta rasu da kuma ƴaƴansa sun samu rauni wanda hakan ya sa ya garzaya domin bayar da rahoto ga ƴan sanda.

Ko da yan sanda suka samu rahoton, sai suka haɗa kai da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS har ta kai ga sun kama Abdulsamad Suleiman.

Bayan gudanar da bincike Abdulsamad ya shaida wa ƴan sandan cewa ya sayar da wayoyi biyu kan naira dubu 12 sa'annan ɗayar wayar kuma ya bai wa wani abokinsa mai suna Mu'azzam Lawan ɗan shekara 17.

Ƴan sandan sun ce tuni aka kama Mu'azzam ɗin inda shi ma ya ce ya sayar da wayar kan naira dubu biyu.

Rundunar ƴan sandan ta ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: