BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

'Yan sandan Ghana sun kama matar da ake zargi ta datse kan mijinta

 120813899 Fa35929d 7906 44ee 8bce 945f545c0143 Ƴan sandan Ghana sun tabbatar da kama matar mai shekaru 27

Mon, 4 Oct 2021 Source: BBC

Rundunar ƴan sandan Ghana reshen yankin gabas ta kama wata mata da ake zargin ta fille kan mijinta bayan sun samu wani saɓani tsakaninsu.

Ƴan sandan Ghana sun tabbatar da kama matar mai shekaru 27.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan reshen jihar gabas DSP Enenezer Tetteh ya ce, lamarin ya faru ne a wani ƙauye mai suna My God Villa Tei Global kusa da wani kauyen manoma da ke gundumar Fantekwa a jihar gabas.

Lokacin da yake bayani a tashar rediyo ta Star FM DSP Eebenezer ya ce ana zargin matar mai suna Rache Tettey da datse kan mijinta Lartey Daniel mai shekaru 35 bayan wata gardama da ta shiga tsakaninsu.

Ya ce bayan sun samu labarin ne al'amarin a ranar Lahadi suka tura jami`ansu don gudanar da bincike.

Ya ce sun tarar da gawar a gefe babu kai, mamacin yana sanye da wando ruwan toka da farar riga ya yi rub da ciki jina-jina kan hanyar wata gona.

DSP Enenezer Tetteh ya ce sun kama matar yayin da aka ajiye gawar mijin a wurin ajiye gawawwaki don tabbatar da sanadiyar mutuwarsa.

Ƴan sandan sun ce ana zargin matar ta yi amfani da ne da adda, inda yanzu take hannun ƴan sanda har sai an kammala bincike.

Babu dai wani cikakken bayani game da al'amarin musamman game da saɓani tsakanin ma'auratan da ya yi sanadin mutuwar mijin.

Ƴan sandan Ghana kuma ba su bayyana cewa matar ta amsa laifin da ake zarginta ba.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: